Kamfanonin Uruguay Sun Zo Kasar Sin Don Cin Gajiyar Kasuwanninta
[ad_1]
A gun dandalin tattaunawa kan zuba jari da hadin gwiwar cinikayya a tsakanin Sin da Uruguay a ranar 3 ga wannan wata, ‘yan kasuwa na kasashen biyu sun yi tattaunawa cikin jin dadi. Abin ban sha’awa a wurin shi ne dukkan ‘yan kasuwa daga kasar Uruguay sun bude Wechat.
A cikin minti 10, an samu sabbin abokai 20, wannan ya shaida cewa, ana da kyakkyawar makoma kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Uruguay. Kasar Uruguay wacce take yankin nahiyar Amurka ta Kudu, tana albarkatun aikin noma da kiwon dabbobi. Ana kuma samar da kayayyakin kasar irinsu jar barasa, da naman sa, da kuma madara ga Sinawa. A cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin ta kasance kasa ta farko mafi yin cinikayya da kasar Uruguay.
Direktar gudanarwa ta hukumar sa kaimi ga zuba jari da fitar da kayayyaki ta karni na 21 ta kasar Uruguay Mariana Ferreira ta bayyana cewa, sun san bukatun kamfanonin Sin na gudanar da ayyuka a kasashen waje, kuma kasar Uruguay tana maraba da kamfanonin Sin da su zo kasar Uruguay su zuba jari da gudanar da ayyuka. A ganinta, ana da kyakkyawan fata ga kamfanonin kasar Uruguay da su zo kasar Sin zuba jari. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link