Yakin Amurka/Israila Da Iran: MDD Ta Yi Gargadin Mutum Miliyan 45 Za Su Fuskanci Karanci Abinci

[ad_1]

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, ko shakka babu, miliyoyin mutane za su fuskanci matsananciyar yunwa, idan har yakin Amurka da Isra’ila a kan Iran ya ci gaba da kuma yadda Iran ta ke mayar da martani.

“Idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba har zuwa watan Yuni, za a iya tura karin mutane miliyan 45 cikin matsananciyar yunwa ta hanyar hauhawar farashin kayayyaki,” in ji Carl Skau, Mataimakin Babban Daraktan Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), wanda ya bayyana hakan a ranar Talatar da ta gabata.

  • Jajircewar Cardoso Wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Nijeriya
  • Aikin Zamantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya Zai Rage Wa Kasa Asasar Naira Tiriliyan Daya —Dantsoho

“Wannan zai haifar  da wani mataki na karuwar yunwa a duniya fiye da kowane irin lokaci tarihi,” in ji Skau.

Hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, wanda ya fara a ranar 28 ga watan Fabrairu, ya danne muhimman hanyoyin bayar da agajin jin kai tare da jinkirta jigilar kayayyaki na ceton rai zuwa wasu munanan rikice-rikice a duniya.

Skau ya ce, farashin jigilar kayayyaki ya karu da kashi 18 cikin dari tun bayan da aka fara yakin, sannan kuma dole ne a samar da wasu hanyoyin.

Ya kara da cewa, karin kudin na zuwa ne sama da raguwar kashe kudade da WFP ke yi, yayin da masu bayar da taimako suka fi maida hankali a kan tsaro.

A Gaza, mazauna yankin na gaggawar tara kayayyaki a yayin da ake rufe kan iyaka da kuma yakin Iran da ke kara samar da karancin kayan masarufi, yayin da karancin kayayyaki ke kara ta’azzara a yankin da aka yi wa kawanya, yayin da Isra’ila ke ci gaba da yakin kisan kare dangi a can.

Isra’ila za ta sake bude wani bangare na mashigar Rafah ta Gaza da Masar a ranar Laraba, wanda ya kawo karshen rufewar makwanni biyu da ta yi, wanda ya dada zurfafa rikicin jin kai a yankin da ya lalace.

Isra’ila ta rufe mashigar a wannan rana, sannan kuma Amurka ta kai hare-hare kan Iran, saboda dalilai na tsaro.

Daraktan yanki na Hukumar Lafiya ta Duniya na Gabashin Bahar Rum, ya yi gargadin a makon da ya gabata cewa, kusan manyan motoci 200 ne ke shiga Gaza a kowace rana, wanda ya yi kasa da kiyasin da ake bukata na yau da kullum na 600.

A halin da ake ciki, sama da mutane miliyan 21 a Sudan, kusan rabin al’ummar kasar na fuskantar matsananciyar yunwa. An tabbatar da cewa, ana fama da yunwa a yankunan da aka kwashe watanni ana gwabzawa, ya sanya ba za a iya kai wa ga ma’aikatan agaji ba.

A watan Janairu, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, agajin da ake bai wa Sudan zai iya karewa cikin ‘yan watanni, matukar ba a yi alkawarin karin daruruwan miliyoyin daloli ba.

Tsawon shekara uku da aka kwashe ana gwabza kazamin yaki tsakanin gwamnatin mulkin soja da dakarun sa kai na gaggawa, ya yi sanadiyyar kisan dubunnan mutane tare da raba kimanin mutum miliyan 14 da muhallansu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *