’Yansanda Sun Ceto Wani Malamin Addini Da Matasa Suka Tsare A Jihar Gombe

[ad_1]

Jami’an  ‘yansanda a Jihar Gombe sun ceto wani malamin addini da wasu matasa suka kulle a cikin gida a kauyen Birin Fulani da ke Karamar Hukumar Nafada.

Rundunar ’yansandan jihar ta ce malamin, mai suna Abubakar Mahmoud Puma, mai shekaru 58 daga Karamar Hukumar Akko, an ceto shi cikin koshin lafiya bayan wasu matasa da ake zargin mambobin wata kungiya ne suka kulle shi a cikin wani gida.

  • Wang Yi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Ministar Harkokin Wajen Birtaniya
  • Aikin Zamantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya Zai Rage Wa Kasa Asasar Naira Tiriliyan Daya —Dantsoho

Kakakin rundunar ’yansandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na safiyar ranar 15 ga Maris, 2026, bayan rundunar ta samu rahoton tashin hankali a cikin al’ummar Birin Fulani.

“Ranar 15/03/2026 da misalin karfe 0300, rundunar ta samu rahoton tashin hankali da barazanar karya zaman lafiya a Birin Fulani da ke Karamar Hukumar Nafada,” in ji Abdullahi.

Ya bayyana cewa jami’in ’yansandan yankin (DPO) ya gaggauta tura tawagar jami’ai zuwa wurin domin dawo da zaman lafiya.

“Da isarsu wurin, an gano cewa wani Abubakar Mahmoud Puma, mai shekaru 58 daga Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe, wasu fusatattun matasa sun kulle shi a cikin gida, bisa zargin cewa ya yi kalaman cin zarafi da batanci ga shugabanninsu,” in ji sanarwar.

Abdullahi ya kara da cewa an tura malamin zuwa yankin ne domin gudanar da Tafsir na watan Ramadan na shekarar 2026, wanda hedikwatar kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatus Sunnah ta kasa da ke Jos ta tura shi.

Ya ce jami’in ’yansandan yankin ya tattauna da matasan da suka fusata, lamarin da ya kai ga ceto malamin lafiya.

“Jami’in ’yansandan yankin ya tattauna da matasan cikin hikima. Bayan wannan shiga tsakani, matasan suka ba da hadin kai, aka ceto malamin lafiya ba tare da ya ji rauni ba. Ba a rasa rai ba kuma an dawo da zaman lafiya a yankin,” in ji shi.

A halin yanzu, kwamishinan ’yansandan jihar, Umar Ahmed Chuso, ya ba da umarnin a gudanar da bincike a boye domin gano musabbabin faruwar lamarin.

“Kwamishinan ’yansandan ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin da suka jawo faruwar lamarin da kuma tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci hukunci bisa doka,” in ji Abdullahi.

Rundunar ’yansandan ta kuma gargadi jama’a da su guji yada labaran karya ko wadanda ba a tabbatar da su ba a shafukan sada zumunta.

“Rundunar na jan hankalin jama’a da su guji wallafa ko yada labaran karya ko marasa tabbaci da ka iya haifar da tashin hankali ko rudar da jama’a,” in ji sanarwar.

Har ila yau, rundunar ta tabbatar wa mazauna Birin Fulani da ma daukacin Jihar Gombe cewa an shawo kan lamarin, tare da kira ga jama’a da su rika bin hanyoyin doka wajen gabatar da koke-kokensu maimakon daukar matakan da ka iya tayar da hankalin jama’a ko karya zaman lafiya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *