ADC – Jafaru Sani Ya Mika Sakon Barka Da Sallah, Ya Soki Tsare El-Rufai

[ad_1]

Mataimakin Shugaban jamiyar ADC (Arewa maso Yamma) Mallam Jafaru Muhammed Sani, ya aika da sakon barka da Sallah ga Musulmai a fadin Nijeriya, yana kira da a ci gaba da zaman lafiya da juriya da fuskantar kalubalen kasa.

A cikin sakon sa na barka da Sallah wanda ya zo bayan kammala Azumin Ramadan, Mallam Sani ya jaddada muhimmancin sadaukarwa, tausayi da hadin kai da wannan wata mai alfarma ya koyar.

  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Na “Sin A Yanayin Bazara” A Brazil
  • Manyan Darussan Kwaikwayo Daga Kyawawan Dabarun Ci Gaban Kasar Sin

Ya yi addu’a ga ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya, yana kira ga ‘yan kasa da su ci gaba da kasancewa masu fata yayin da ADC ke shirin tunkarar zabubbukan 2027.

Baya ga sakon barka da Sallah, Sani ya yi karin suka kan abin da ya kira “tsarewar da ba ta dace ba” da aka yi wa Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, kuma babban jigo a jam’iyyar ADC. Ya yi kira ga kotuna da hukumomin gwamnati da su tabbatar da adalci da bin doka, yana gargadin cewa tsare ‘yan adawa ba bisa ka’ida ba na iya lalata dimokuradiyya kuma ya nuna alamar karkata zuwa mulkin kama-karya.

“ADC ta yi Allah wadai da wadannan ayyuka matuka,” in ji Sani, yana jaddada cewa dimokuradiyya tana bunkasa ne bisa girmama ‘yancin dan adam, bin doka da kuma jure ra’ayoyi daban-daban.

Ya kuma karfafa ‘yan Nijeriya, musamman magoya bayan ADC, da su shiga cikin aikin rajistar mambobi da jam’iyyar ke gudanarwa, tare da tabbatar da cewa tarukan mazabu, kananan hukumomi da na jihohi za su gudana cikin lumana da gaskiya.

“A yayin da muke bikin wannan Sallah, mu sabunta alkawarinmu ga adalci, dimokuradiyya da hadin kai,” in ji Sani. “Tare, za mu iya gina Jihar Kaduna da Nijeriya da za su nuna burin da fata na al’ummarta.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *