Delcy Rodríguez ta sauya manyan hafsoshin sojin Venezuela

[ad_1]



Shugabar riƙo ta ƙasar Venezuela, Delcy Rodríguez, ta sanar da sauya dukkan manyan hafsoshin rundunar sojin ƙasar, a wani sabon mataki na gyare-gyare tun bayan kifar da tsohon shugaban ƙasa Nicolás Maduro da Amurka ta yi.

Rodríguez ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na sada zumunta, inda ta ce ta naɗa sabuwar rundunar manyan hafsoshin soji domin tafiyar da harkokin tsaro a ƙasar.

Matakin na zuwa ne kwana guda bayan ta sallami ministan tsaron ƙasar, Janar Vladimir Padrino wanda ke da kusanci da Maduro, tare da maye gurbinsa da tsohon shugaban hukumar leƙen asiri, Janar Gustavo Gonzalez Lopez.

Tun bayan kama Maduro da sojojin Amurka suka yi a watan Janairu, gwamnatin riƙon ƙwarya ƙarƙashin Rodríguez ke ƙoƙarin daidaita al’amuran ƙasar da ke fama da matsanancin koma bayan tattalin arziki da ƙarancin abinci da magunguna.

A halin yanzu, Rodríguez na fuskantar ƙalubale tsakanin bayar da kai bori ya hau ga matsin lambar Amurka da kuma gamsar da magoya bayan tsohon shugaban, yayin da sojojin ƙasar ke da muhimmiyar rawa a fannoni da dama, ciki har da harkokin mai, kasuwanci da rarraba abinci.

Rahotanni sun ce sauye-sauyen na daga cikin yunƙurin ƙarfafa ikon gwamnati a kan rundunar soji, wadda ke taka muhimmiyar rawa a siyasa da tattalin arzikin ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *