Kasar Sin: Kashe Shugabanni Da Hare-Hare Kan Fararen Hula A Iran Abu Ne Da Ba Za A Lamunta Ba
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce kashe shugabannin Iran da kai hare-hare kan fararen hula da kayayyakinsu, abu ne da ba za a taba lamunta ba.
Kakakin ma’aikatar Lin Jian ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da amsa a taron manema labarai na yau Alhamis, inda ya ce kasar Sin ta kasance mai adawa da amfani da karfi a harkokin da suka shafi dangantakar kasa da kasa. Kafin sannan, rahotanni sun sanar da mutuwar Ali Larijani, sakataren majalisar koli kan tsaron kasar Iran, sanadiyyar hare-haren Isra’ila.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta kadu da irin furucin da Isra’ila ta yi cewa, ta sahalewa sojojinta kai farmaki da kashe duk wani jami’in kasar Iran, ba tare da bukatar neman izini ba.
Lin Jian ya ce kasar Sin na kira ga bangarorin da ke rikicin, su dakatar da farmakin soja nan take tare da kaucewa jefa yankin cikin yanayin da za a kasa shawo kansa.
Har ila yau yayin taron manema labaran, Lin Jian ya yi bayani kan ziyarce-ziyarce na baya bayan nan da wakilin musammam na Sin kan yankin Gabas ta Tsakiya, Zhai Jun ya yi a wasu kasashen yankin, inda ya ce dukkan bangarorin sun yabawa matsayar rashin nuna bangaranci ta kasar Sin, da kokarinta na wanzar da zaman lafiya. Ya ce Sin babbar kasa ce da ta san ya kamata, kuma sahihiyar abokiya ga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya. Bugu da kari, ya ce muddun rikicin ya ci gaba, to kasar Sin ma ba za ta yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da shiga tsakani ta hanyar diflomasiyya da nufin kawo karshensa ba. (FMM)