Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda sama da 61 a Borno
[ad_1]
Rundunar Sojin Najeriya ta Operation Hadin Kai (OPHK), tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Sama (NAF), sun kashe ’yan ta’addan ISWAP sama da 61 bayan sun yi yunƙurin kai hari yankin Malam Fatori da ke Ƙaramar Hukumar Abadam a Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai harin ne da safiyar ranar Laraba.
Sun shiga garin da ƙafa sannan suka yi amfani da jiragen sama marasa matuƙa domin ƙoƙarin karya tsaron sansanin Bataliya ta 68.
Rahotanni sun ce maharan sun shiga ta ɓangaren Kamfanin Bravo daga yankin Duguri, amma sojoji suka yi musu ɓarin wuta.
A cewar majiyar tsaro, sojojin da suka samu goyon bayan hare-hare ta sama sun gwabza faɗa mai tsanani da ’yan ta’addan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mahara da dama.
Majiyar ta ƙara da cewa haɗin kai tsakanin sojin sama da na ƙasa ya taimaka wajen gano wuraren da ’yan ta’addan suke.
“Mun kai hare-hare ta sama sau huɗu kan wuraren da ’yan ta’addan suka taru, wanda hakan ya rage karfinsu sosai,” in ji majiyar.
Ta ce wannan haɗin gwiwa ya hana ’yan ta’addan zirga-zirga, tare da tilasta musu janyewa cikin ruɗani zuwa yankin Arege bayan sun ruwan wuta.
Hakazalika, majiyoyin sun bayyana cewa jiragen yaƙin Nijar sun bayar da gudunmawa wajen ƙara matsa wa ’yan ta’addan da suka tsere, kodayake ana ci gaba da tantance asarar da suka yi.
“Rundunar haɗin gwiwa daga Jamhuriyar Nijar ta kai farmaki cikin gaggawa don tallafa wa wannan aiki, wanda ya ƙara tsananta matsin lamba ga ’yan ta’addan,” in ji majiyar.
Dangane da ɓangaren sojoji kuwa, an ce sojoji huɗu sun ji rauni.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link