Kasar Sin Na Son Taimaka Wa Habasha Sake Gina Yankunan Da Ibtila’in Zaizayar Kasa Ya Shafa
[ad_1]
Rahotannin sun ruwaito cewa, mamakon ruwan sama da aka yi a kudancin kasar Habasha ya janyo ibtila’in zaizayar kasa tare da zabtarewar laka, al’amarin da ya yi ajalin mutane akalla 100, kuma akwai kimanin 60 da har yanzu ba a ji duriyarsu ba, kana, ya tilasta wa mutane kusan 3500 barin matsugunansu. Gwamnatin kasar ta sanar da zaman makoki daga ranar 14 zuwa 16 ga watan Maris da muke ciki, tare da saukar da tuta zuwa rabin sanda a duk fadin kasar.
Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lin Jian ya bayyana a yau Talata 17 ga wata cewa, kasarsa ta yi alhinin wadanda suka rasa rayukansu, tare da jajanta wa iyalan mamatan. Kuma Sin tana da yakinin cewa, a karkashin jagorancin gwamnatin Habasha, mutanen da ibtila’in ya shafa za su iya shawo kan lamarin tare da sake gina matsugunansu. Haka zalika, kasar Sin na son samar da taimako gwargwadon iyawarta ga mutanen da ibtila’in ya shafa wajen sake gina matsugunansu, bisa bukatun kasar Habasha. (Murtala Zhang)
[ad_2]
Source link