Shugaban Hukumar Yaƙi da Ta’addanci na Amurka ya ajiye aiki saboda rashin goyon bayan yaƙin Iran
[ad_1]
Shugaban Hukumar Yaƙi da Ta’addanci ta Amurka, Joe Kent ya ajiye aikinsa a wannan Talatar saboda abin da ya kira rashin goyan bayan yaƙin da ƙasar ke yi da Iran.
A wasiƙar da ya rubuta ta murabus ɗinsa, Kent ya bayyana cewar Iran ba ta yi wa ƙasar Amurka wata barazana ba, saboda haka babu dalilin afka mata da yaƙi kamar yadda Shugaba Donald Trump ya ba da umarni.
Kenta ya ce babu dalilin da zai sa a cikin hankalinsa ya goyi bayan wannan yaƙin na Iran da ake ci gaba da yi, domin babu wata barazanar da ta ke yi wa ƙasar su.
Haka kuma, ya ce ta tabbata ƙarara cewar sun shiga yaƙin ne saboda Isra’ila da masu goya mata baya.
“Iran ba ta barazana ga ƙasarmu, kuma a bayyane take cewa mu ne muka fara wannan yaƙi saboda matsin lamba daga Isra’ila da masu neman mata gindin zama masu ƙarfin faɗa a ji.
“Ina goyon bayan aƙidu da tsare-tsaren ƙasashen waje da ka yi kamfe da su a 2016 da 2020 da 2024 waɗanda kuma ka ɗabbaƙa a zangon mulkinka na farko.
“Har zuwa watan Yunin 2025, ka fahimci cewa yaƙe-yaƙe a Gabas ta Tsakiya tarko ne aka ɗana wa Amurka na ƙarar da rayukan Amurkawa da arziƙi da cigaban ɗorewar ƙasarmu.
“A matsayina tsohon soja wanda ya je yaƙe-yaƙe har sau 11 kuma mutumin da ya rasa matarsa a yaƙin da Isra’ila da ƙirƙira, babu yadda za a yi na goyi bayan aikewa da matasa domin yin faɗa da ba zai amfani Amurka ba..”
Kent ya yi suna wajen goyan bayan shirin Trump na ‘America First’, amma kuma ya bayyana adawar shi da duk wani shiri na amfani da sojojin ƙasar a ƙasashen ƙetare.
Wasu masana sun bayyana cewar a bisa dokokin duniya, barazanar kai wa ƙasar hari ne kawai zai sa ta ƙaddamar da yaƙi.
A wata hira da manema labarai, Trump ya martani kan matakin da Kent ya ɗauka, inda ya ce ya daɗe yana “ɗaukarsa a matsayin mutum mai rauni ta fuskar tsaro.”
A cewar Trump, “abu ne mai kyau da (Kent) ya ajiye aiki, in dai har zai iya buɗe baki ya ce ƙasar Iran ba ta barazana ga Amurka.
“Iran barazana ce kuma kowace ƙasa ta gano irin barazanar da ke tattare da ƙasar Iran, a cewar Trump kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link