Dalilin da ƙasashen Turai suka yi wa Trump tawaye kan shiga yaƙin Iran

[ad_1]



An samu ƙarin wasu shugabannin Turai da suka yi wa Shugaban Amurka Donald Trump tawaye kan buƙatarsa ta neman taimako wajen tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz da Iran ta rufe.

Tuni dai manyan ƙasashe kamar Jamus, Faransa da Birtaniya suka bayyana cewa ba za su shiga yaƙin ba, suna mai jaddada cewa rikicin ba ya ƙarƙashin dokokin tsaron haɗin gwiwa na NATO.

Bayan wani taron ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai, babbar jami’ar kula da manufofin ƙasashen waje ƙungiyar, Kaja Kallas, ta ce “babu wanda ke son yin hakan” inda ta ƙara da cewa “wannan ba yaƙi ba ne na ƙasashen Turai.”

Shi ma shugaban Finland, Alexander Stubb, ya shaida wa BBC cewa Mista Trump ne da kanshi ya yanke shawarar ƙaddamar da yaƙi kan Iran ba tare da shawarar kowa ba, don haka kamata ya yi ya lalubo bakin zaren warware matsalar da ƙashin kansa.

Aminiya ta ruwaito shi ma shugaban gwamnatin Jamus Friedrick Merz, yana cewa yaƙin na Iran ba batu ne da ya shafi ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO ba, yayin da mahukunta a Paris, suka fito ƙarara, suka shaida wa Trump cewa ba za su aika dakarunsu Mashigar Hormuz ba.

Shugaban Gwamnatin Jamus ya ce babu wata yarjejeniya ta duniya ko ta NATO da za ta halatta shiga yaƙin, yana mai nanata cewa ƙasarsa ba za ta shiga ba kwata-kwata.

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya nuna cewa ƙasarsa ba za ta shiga yaƙin kai tsaye ba, sai dai tana neman mafita ta hanyar tattaunawa da sulhu.

Kazalika, Firaministan Girka, Kyriakos Mitsotakis, ya bayyana cewa Turai ba za ta shiga duk wani aikin soja da Iran ba, duk da matsin lambar da shugaban Amurkan ke yi.

Mitsotakis ya ce maimakon shiga yaƙi, ya kamata Turai ta fi mayar da hankali kan illar tattalin arziki da rikicin ke haifarwa, musamman tashin farashin man fetur da dizal a duniya.

Matakin na Mitsotakis ya yi daidai da matsayar sauran ƙasashen Turai da suka ƙi amsa kiran Trump na tura sojoji domin buɗe Mashigar Hormuz.

Rahotanni sun kuma nuna cewa ƙasashe irin su Italiya da Japan da Australia sun bi sahun Turai wajen ƙin shiga yaƙin, duk da cewa Amurka na ƙoƙarin jan hankalinsu su taimaka wajen buɗe Mashigar Hormuz.

Sai dai Trump kamar yadda jaridar Financial Times ta ruwaito ya yi gargaɗin cewa makomar NATO na iya zama cikin haɗari idan ƙawayen Amurka ba su bayar da goyon baya ba.

Matakin na Turai ya nuna yadda rikicin Iran ke ƙara raba kan ƙasashen yamma, inda wasu ke kallon yaƙin a matsayin wanda Amurka da Isra’ila suka fara, ba tare da cikakken goyon bayan ƙawayensu ba.

Tun da farko a Fadar White House, Shugaba Trump ya caccaki ƙasashen duniya, da ya ce sun ja baki sun yi shiru a kan shirin nasa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *