Mutum 6 sun rasu, ’yan Najeriya sun jikkata bayan Iran ta sake kai hari UAE
[ad_1]
Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da sama da mutum 140 suka jikkata bayan Iran ta sake kai hari da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
Rahotanni sun bayyana cewar wasu ’yan Najeriya na daga cikin waɗanda suka jikkata a harin.
Ma’aikatar Tsaron UAE, ta bayyana cewa na’urorin kariyarta na sararin samaniya sun yi nasarar kakkaɓo wasu daga cikin makamai masu linzami da jiragen marasa matuƙa da Iran ta harba a ranar 14 ga watan Maris.
Hukumomi sun bayyana wannan harin matsayin ta’azzara rikici a rikicin Gabas ta Tsakiya.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta bayyana cewa dakarunta sun tare makamai masu linzami guda tara da kuma jirage marasa matuƙa 33 yayin harin.
“Na’urorin kariyarmu na sararin samaniya sun kakkaɓo makamai masu linzami guda tara da jirage marasa matuƙa 33 da aka harbo daga Iran a ranar 14 ga watan Maris,” in ji ma’aikatar.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Tun farkon fara wannan harin na Iran, an tare jimillar makamai masu linzami 294, da wasu makamai 15, da kuma jirage marasa matuƙa 1,600.”
Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane shida da raunata wasu 141, ciki har da baƙi da aiki a UAE.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da ’yan asalin UAE da kuma ’yan ƙasashen Pakistan, Nepal, da Bangladesh.
Haka kuma, an tabbatar da jikkatar wasu ’yan Najeriya mazauna ƙasar.
Duk da cewa ma’aikatar ba ta bayyana takamaiman wuraren da harin ya shafa ba, ta tabbatar da cewa mutane daga ƙasashe daban-daban sun jikkata.
Ana kyautata zaton Iran ta kai wannan hari ne a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan wasu sansanoninta a kwanakin baya.
Rahotanni sun nuna cewa Iran ta kuma kai wasu hare-haren ƙasashe irin su Saudiyya da Qatar, inda ta lalata wasu gine-gine.
Ƙasar UAE na ɗaya daga cikin ƙasashen da ’yan Najeriya da dama ke zuwa domin yin aiki, kasuwanci, ko kuma yada zango kafin wucewa zuwa wasu sassan duniya.
A halin yanzu, wasu ’yan Najeriya da ke maƙale a ƙasashen Gabas ta Tsakiya sun yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta shirya yiwuwar kwashe su idan har yanayin tsaro ya ci gaba da taɓarɓarewa.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abdur-Rahman Balogun, ya bayyana cewa an riga an kwashe wasu ’yan ƙasar daga Iran.
“Jami’an ofishin jakadancin Najeriya a Iran sun raka wasu ’yan Najeriya da suka buƙaci ficewa zuwa iyakar Armenia domin su tsallaka cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.
Hukumomi sun kuma ƙara da cewa kawo yanzu babu wani ɗan Najeriya a Iran da ya samu matsala kai-tsaye sakamakon yaƙin.
Hakazalika, jami’an gwamnati na ci gaba da kasancewa a iyakokin ƙasar domin bayar da taimako ga duk wanda ke son ficewa daga Iran.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link