Yara miliyan 6.4 na fama da matsanancin rashin abinci a Arewacin Najeriya — ICRC
[ad_1]
Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Duniya, International Committee of the Red Cross (ICRC), ta bayyana damuwa kan ƙaruwar matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a yankunan da ke fama da rikici a Arewacin Najeriya.
Ƙungiyar ta ce kimanin yara miliyan 6.4 ’yan ƙasa da shekara biyar a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ne ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.
A cewar ƙungiyar, rikicin da aka shafe kusan shekara 15 ana yi ya lalata rayuwar jama’a, noma da samar da abinci, wanda ya sa magidanta da dama suka rasa isasshen abinci.
A wata cibiyar kula da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki a Damaturu da ke Jihar Yobe, wata uwa mai suna Zainab Isa ta kawo ɗanta ɗan watanni 22, Umar, wanda jikinsa ya kumbura saboda matsanancin rashin abinci mai gina jiki.
Bayan an kwantar da shi a asibiti tare da ba shi abinci mai gina jiki da magani, lafiyarsa ta fara inganta cikin mako guda.
A Biu da ke kudancin Jihar Borno, wata mata mai suna Fatima ta ce tana shan wahala wajen ciyar da ’ya’yanta 13 bayan rikicin ’yan ta’adda ya tilasta musu barin gidansu da gonakinsu.
ICRC, ta ce tana kula da yara sama da 1,000 masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a kowace shekara.
Sannan tana kula da lafiyar yara da tallafin noma, samar da ruwan sha mai tsafta da kuma tallafin kuɗi ga magidanta masu rauni.
Ƙungiyar ta ce a shekarar 2025, sama da mutum 348,000 sun samu magani kan matsanancin rashin abinci mai gina jiki a cibiyoyin lafiya da ta ke tallafawa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
Sai dai duk da wannan taimako, ƙungiyoyin agaji sun yi gargaɗin cewa matsalar na ci gaba da ƙamari saboda matsalar tsaro da kuma raguwar hanyoyin samun kuɗin shiga a yankin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link