Tambuwal ya koma jam’iyyar ADC

[ad_1]



Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Kudu a Majalisar Dattawa, Aminu Waziri Tambuwal, ya koma jam’iyyar ADC, bayan ya fice daga PDP.

A cikin wata sanarwa da ofishinsa na yaɗa labarai ya fitar.

Tambuwal ya ce ya yanke shawarar komawa ADC ne saboda Najeriya na buƙatar jam’iyya mai ƙarfi wadda ta ginu a kan gaskiya, haɗin kai, riƙon amana da kuma jajircewa wajen bunƙasa ƙasa.

Ya kuma jaddada ƙudirinsa na ci gaba da yi wa Najeriya hidima tare da goyon bayan dimokuraɗiyya da haɗin kan ƙasa.

Tsohon gwamnan na Jihar Sakkwato, ya riga ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya alaƙnta ficewarsa da rikice-rikicen cikin gida, saɓanin ra’ayi a shugabanci da kuma rabuwar kai.

A cewarsa, waɗannan rikice-rikice sun raunana haɗin kai da kuma alƙiblar da aka gina jam’iyyar PDP a kai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *