Ina da yaƙinin sabon jagoran Iran zai ɗora daga inda mahaifinsa ya tsaya — Putin
[ad_1]
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa yana yaƙinin cewa sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, zai ɗora daga inda mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei ya tsaya.
Putin ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon taya murna da aka wallafa a shafin Kremlin, inda ya tabbatar da goyon bayan Rasha ga Iran a wannan lokaci da ƙasar ke fuskantar hare-hare.
“Ina miƙa gaisuwa ta musamman tare da taya Mojtaba Khamenei murna kan naɗinsa a matsayin jagoran addinin Iran,” in ji Putin.
Ya ƙara da cewa Rasha za ta ci gaba da kasancewa abokiyar Iran mai aminci tare da ba ta goyon baya ba tare da wata shakka ba.
Putin ya ce yana da yaƙinin cewa sabon jagoran zai ɗora daga inda mahaifinsa ya tsaya cikin girmamawa, tare da haɗa kan al’ummar Iran a wannan mawuyacin lokaci.
“A wannan lokaci da Iran ke fuskantar manyan hare-hare, tabbas za a buƙaci ƙarfin zuciya da sadaukarwa.
“Ina da yaƙinin cewa za ka ci gaba daga inda mahaifinka ya tsaya cikin girmamawa kuma ka haɗa kan al’ummar Iran a wannan mawuyacin lokaci,” in ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa, majalisar ƙoli ta malaman addini ta Iran, wadda ta ƙunshi mutum 88 kuma take da alhakin naɗa manyan jami’an addini da na siyasar ƙasar bisa kundin tsarin mulkin ƙasar, ce ta zaɓi Mojtaba Khamenei mai shekara 56 a ranar Lahadin da ta gabata.
Da naɗinsa, Mojtaba ya zama jagoran addinin Iran na uku tun juyin juya halin shekarar 1979, inda ya zama shugaba a wani mawuyacin lokaci na yankin Gabas ta Tsakiya da kuma rashin tabbas a cikin ƙasar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link