’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace wasu 5 a Sakkwato
[ad_1]
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari ƙauyen Mallamawar Yari da ke Ƙaramar Hukumar Rabah a Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutum daya tare da sace wasu biyar.
Harin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi lokacin da maharan suka shiga ƙauyen suka fara harbe-harbe.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar harin.
Sai dai ya ƙaryata rahotannin da ke cewa maharan sun sa hijaban mata wajen kai harin.
“Ba gaskiya ba ne cewa ’yan bindigar sun sa hijaban mata. Sun shigo ƙauyen ne da yawa sannan suka fara harbe-harbe,” in ji Rufa’i.
’Yan sanda sun ce mutum ɗaya ne ya mutu a harin, yayin da aka sace mutane biyar; mata uku da maza biyu.
Wata majiyar tsaro ta ce maharan sun zo da yawa a kan babura kusan 30, kuma kowane babur na ɗauke da ’yan bindiga uku.
“An sanar da mu game da harin, kuma mun yi ƙoƙarin daƙile su, amma sun fi mu yawa. Mu biyar ne kawai jami’ai, yayin da su kuma suka zo da babura da yawa,” in ji majiyar.
Majiyar ta ƙara da cewa jami’an tsaro sun ga maharan suna tafiya da waɗanda suka sace, amma ba za su iya fafatawa da su ba saboda sun fi su yawa.
Ta kuma bayyana cewa kwanakin suka gabata an kai wani makamancin hari a wani ƙauye, amma jami’an tsaro sun samu nasarar fatattakar maharan, tare da kashe ɗaya daga cikinsu sannan suka ƙwato makamai.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link