Trump ya zargi Iran da kai hari makaranta a Kudancin ƙasar

[ad_1]



Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi Iran da kai harin da hukumomin ƙasar suka ce ya afka wa wata makarantar firamare ta ‘yan mata a kudancin ƙasar.

Trump ya bayyana haka ne ga manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One, inda ya ce suna zargin Iran ne saboda yadda makaman da take amfani da su ba su da cikakken daidaito.

“Muna tunanin Iran ce ta kai harin da kanta, saboda makaman da take amfani da su ba da nagarta da ingancin kai hari kan ainihin inda suka nufa,” in ji Trump.

Rahotanni daga hukumomin Iran sun ce harin ya auku ne a wata makarantar firamare ta ‘yan mata a yankin Minab, inda aka ce sama da mutum 150 suka mutu, yawancinsu dalibai.

Sai dai har yanzu babu wata ƙasa da ta ɗauki alhakin harin. Amurka da Isra’ila sun ce har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin, yayin da Iran ke zargin ƙasashen biyu da hannu a kai.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ce bai samu damar kai ziyara wurin da abin ya faru ba domin tabbatar da lamarin, haka kuma babu tabbacin adadin waɗanda suka mutu daga wata majiya mai zaman kanta.

A wani ɓangare, dakarun juyin-juya hali na Iran IRGC sun ce sun kai hari kan sansanin sojin Amurka na Al Dhafra da jiragen yaƙi marasa matuƙa da makamai masu linzami, suna zargin cewa an yi amfani da sansanin wajen kai harin.

Ma’aikatar tsaron Amurka, ta tabbatar da cewa ana binciken lamarin, yayin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce Amurka ba za ta kai hari da gangan kan makaranta ba.

Jaridar The New York Times ta rawaito cewa bayanan sojojin Amurka na nuna cewa hare-haren da ake kai wa kan wasu wuraren sojin ruwa kusa da Mashigar Hormuz na iya kasancewa suna da alaƙa da harin da ya afka wa makarantar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *