Adadin Zirga-zirgar Matafiya A Cikin Kasar Sin A Shekarar 2025 Ya Haura Miliyan 150

[ad_1]

Ministan ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa na kasar Sin Sun Yeli, ya ce adadin zirga-zirgar matafiya a cikin kasar Sin a shekarar 2025, ya haura miliyan 150, adadin da ya karu da kaso 17 bisa dari a mizanin shekara-shekara, yayin da kuma kudaden da matafiyan suka kashe ya haura dalar Amurka biliyan 130.

Sun Yeli, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Asabar din nan, a gefen taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin dake gudana yanzu haka, ya ce adadin shigowar baki daga wajen kasar ba tare da bukatar biza ba, ya zarce miliyan 30. Kazalika, Sin ta aiwatar da managartan matakai na inganta hidimar biyan kudade na tafi da gidanka, ga baki maziyarta kasar na sassan kasa da kasa.

Ya ce a shekarar ta 2025, alkaluma sun nuna yadda masu yawon bude ido dake shigowa kasar Sin sun kashe kusan yuan biliyan 80, kimanin dalar Amurka biliyan 11.59, ta amfani da hidimomin biyan kudade na tafi da gidanka.

Sun ya ce jumlar “Zama dan kasar Sin” na kara yaduwa a kafofin sada zumunta na zamani, inda karin baki ‘yan kasashen waje ke nuna sha’awar ziyartar kasar Sin. Kuma fannonin da suka fi mararin gani sun hada da tafiye-tafiye ta jiragen kasa masu matukar sauri, da kallon wasannin jirage marasa matuka, da tausa domin magance cututtuka da ake yi bisa salon gargajiyar kasar Sin. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *