Sin Na Yiwa Dukkanin Kasashe Maraba Da Rungumar Manufar Kafa Kawancen GFGG
[ad_1]
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce nasarar kafa kawancen inganta jagorancin duniya ko GFGG a birnin New York, da kuma birnin Geneva, da ma irin ci gaban da aka samu a fannin cikin watanni da dama, ya nuna shawarar inganta jagorancin duniya ko GGI da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ta yi daidai da bukatun duniya da burikan al’umma.
Mao Ning ta bayyana hakan ne a Larabar nan, tana mai cewa turbar wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaban bil Adama na fuskantar tarin kalubale, don haka a yanzu lokaci ne mafi muhimmanci na sake rungumar tushen kafuwar MDD, da nacewa tsarin cudanyar mabambantan sassa a duniya, da kare gaskiya da daidato tsakanin sassan kasa da kasa, da aiki tukuru wajen kare zaman lafiya, da daidaito da ci gaba.
Daga nan sai ta ce kasar Sin na maraba da dukkanin kasashen duniya da suka amince da wannan manufa, kuma ta hanyar kaddamar da kawancen GFGG, Sin a shirye take ta yi aiki tare da sassan kasa da kasa wajen bibiyar hanyoyin sauye-sauye, da kyautata jagorancin duniya, kana za ta yi hadin gwiwa wajen shawo kan tarin kalubalen duniya, da gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link