Za a binne Khamenei a birnin Mashhad

[ad_1]

Za a binne jagoran addini na Iran, marigayi Ayatollah Ali Khamenei a birnin Masshad kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Fars ya ruwaito a ranar Talata.

Khamenei wanda ya jagoranci ƙasar Iran tsawon shekaru 36, ya yi gamo da ajalinsa bayan wani hari da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a ranar Asabar.

Khamenei wanda ya rasu yana da shekaru 86 a duniya, haifaffen birnin Mashhad ne, birni na biyu mafi girma a Iran, inda a nan aka binne mahaifinsa a wurin bauta na Imam Reza.Gabanin binne gawarsa, dandanzon jama’a za su taru domin yi masa jana’izar bankwana a birnin Tehran.

Tun daga yau Laraba ce za a fara gudanar da taron jana’izar Khamenei, a birnin Tehran kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta sanar.

Kafar ta ruwaito cewa za a fara taron da misalin ƙarfe 18:30 na agogon GMT, kuma shirye-shiryen za su gudana na tsawon kwanaki uku kafin a yi jerin gwanon jana’iza.

A yau ɗin ne kuma ake sa ran za a ayyana magajin Khamenei, inda Jaridar NewYork Times ta ambato wasu jami’an Iran na cewa ɗan Khamenei wato Mojtaba Khamenei na daga cikin waɗanda ake ganin suna kan gaba wajen maye gurbinsa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *