Iran ta tabbatar da kishan jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei

[ad_1]



Iran ta tabbatar da cewa an kashe jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan ƙasar a ranar Asabar.

Wannan na zuwa ne bayan an yi tantama kan mutuwar jagoran addinin wanda Shugaban Amurka Donald Trump ya shelanta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

Sai dai kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta ce an kashe jagoran, lamarin da ya sanya kiraye-kiraye ga rundunar juyin-juya-hali ta Revolutionary Guards domin ta ɗauki matakin ramuwar gayya.

Gidan talbijin na ƙasar Iran ranar Lahadi ya sanar da makokin kwana 40 tare da bayar da hutun kwana bakwai bayan kisan shugaban addinin ƙasar mai shekara 86, wanda ke kan mulki tun shekarar 1989.

Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa a kashe ‘yar Ayatollah Ali Khamenei da jikarsa da kuma surukinsa a harin.

“Shahadar da shugaban addini ya yi ba za ta sa a manta da tafarkinsa da jagorancinsa ba, hasali ma, za a tabbatar da su ne bisa ƙarfin gwiwa da jajircewa,” a cewar mai gabatar da labarai a gidan talbijin na gwamnatin Iran.

Rundunar juyin-juya-hali ta Revolutionary Guards ta sha alwashin yin ramuwar gayya kan “wadanda suka kashe” Khamenei.

“Rayuwar gayya da ƙasar Iran za ta yi zai kasance mai tsanani kuma cike da karsashi, sannan waɗanda suka kashe Shugaban Al’umma ba za su ci bulus ba,” in ji wata sanarwa da rundunar juyin-juya-hali ta fitar.

Harin da Isra’ila da Amurka suka kai Iran ranar Asabar ya zo ne a lokacin da Khamenei yake gudanar da taro da manyan masu ba shi shawara, a cewar wsu majiyoyi na gwamnatin Amurka.

Isra’ila ta yi iƙirarin cewa an kashe Khamenei ne tare da manyan na hannun damansa da suka haɗa da Ali Shamkhani, tsohon Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa, da Mohammad Pakpour, kwamandan Rundunar juyin-juya-hali ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC).

Tarihin Ayatollah Khamenei

Ayatollah Ali Khamenei shi ne jagoran addini na Iran na biyu bayan juyin-juya halin ƙasar da aka yi a shekarar 1979, kuma tun a shekarar 1989 yake riƙe da muƙamin.

Matasan ƙasar yawanci sun taso ne suna ganin sa a matsayin jagoran addininsu.

Yana riƙe ne da madafun iko mai ƙarfin gaske – yana da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani matakin ƙasar, sannan yana da ikon zaɓa ko naɗa wanda yake so a wata kujerar mulkin ƙasar.

Shi ne jagoran askarawan ƙasar, ciki har da dakarun juyin juya-halin ƙasar wato Iranian Revolutionary Guard Corps (IRGC).

An haife shi ne a garin Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran a shekarar 1939.

Shi ne na biyu a wurin mahaifansa masu ’ya’ya takwas, kuma mahaifinsa ya kasance malamin Shi’a.

Ya fara karatu ne da koyon karatun Ƙur’ani tun yana ƙarami, inda ya zama malami yana da shekara 11.

Duk da cewa yana daga cikin masu bayar da fatawa kan al’amura, kafin rasuwarsa za a iya cewa aikinsa ya fi tasiri a siyasance.

Khamenei mutum ne da Allah Ya yi wa baiwar iya tsara magana sosai, kuma ya kasance kan gaba wajen sukar gwamnatin Shah ta Iran, sarkin da aka hamɓarar a juyin juya-halin ƙasar.

Yawancin rayuwar Khamenei ta kasance a ƙarƙashin ƙasa ne ko a gidan yari. Sau shida ana kama shi a zamanin mulkin Shah, inda ya fuskanci uƙuba.

Shekara ɗaya bayan juyin juya-hali a 1979, sai Ayatollah Ruhollah Khomeini ya naɗa shi babban limamin Juma’a na birnin Tehran.

Daga baya sai aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 1981, kafin shugabannin addinin ƙasar suka zaɓe shi a shekarar 1989 domin ya maye gurbin Ayatollah Khomeini, wanda ya rasu yana da shekara 86.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *