Haƙuri da juriya ne mabuɗin nasara — Kocin Chelsea
[ad_1]
Kocin Chelsea, Liam Rosenior, ya bayyana cewa yana fatan samun damar da zai daɗe a kulob ɗin domin kawo ƙarshen rashin tabbas ɗin da ƙungiyar ke fuskanta a ‘yan shekarun nan.
Rosenior, wanda a watan Janairun da ya gabata aka ɗauko daga Strasbourg domin maye gurbin Enzo Maresca, ya zama koci na dindindin na biyar a Chelsea tun bayan da masu kamfanin BlueCo suka mallaki ƙungiyar.
Kocin mai shekaru 41 shi ne na tara da ya riƙe muƙamin horar da Chelsea a cikin shekaru shida kacal — a daidai lokacin da Arsenal ta soma samun daidaito a ƙarƙashin Mikel Arteta, ƙungiyar da za ta karɓi baƙuncin Chelsea a wannan Lahadin.
A ’yan shekarun nan, Chelsea ta sha sauye-sauyen ‘yan wasa da jami’an kulob da dama, a yayin da daga cikin ‘yan wasan da suka lashe kofin Zakarun Turai a 2021, Reece James ne kaɗai ya rage zuwa watan Satumbar bara.
Thomas Tuchel, wanda ya jagoranci Chelsea zuwa nasarar lashe babbar gasar ta Turai, tuni aka sallame shi watanni huɗu kacal bayan sabbin masu kulob sun karɓi ragamar iko.
Haka kuma, Graham Potter da Mauricio Pochettino sun yi taƙaitaccen lokaci, sannan shi ma Maresca ya raba gari da ƙungiyar bayan shekara ɗaya da rabi sakamakon saɓani da shugabannin kulob ɗin.
Da aka tambaye shi game da makomarsa a Chelsea, Rosenior ya ce haƙuri da juriya su ne mabuɗin nasara.
Ya ce, “Ina so in daɗe a wannan kujera. Ina so in zama wani ginshiƙi na samun nasara mai ɗorewa tare da ‘yan wasa, ma’aikata da masu kulob ɗin. Wannan ne dalilin da ya sa na amince da wannan ƙalubale.”
Ya ƙara da cewa, “A harkar ƙwallo, abin da ke ke sa ka yi dogon zango ita ce nasara. Dole ne ka nuna ƙwarewa ba a wasa kaɗai ba, har ma a wajen horaswa, taro da inganta ‘yan wasa.”
Rosenior ya bayyana fatan cewa zuwansa zai kawo ƙarshen tababar da ta addabi Chelsea, tare da jaddada aniyarsa ta kai kulob ɗin ga nasarorin da ya dace da su.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link