Yadda yaƙi ya ƙazanta tsakanin Pakistan da Afghanistan

[ad_1]



Pakistan ta kai mummunan hari ta sama kan manyan biranen Afghanistan, ciki har da Kabul, yayin da ƙasashen biyu ke ci gaba da gwabza faɗa tsakaninsu.

Kakakin gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya tabbatar da cewa hare-haren sojojin Pakistan ɗin sun faɗa kan Kabul babban birnin kasar, sai Kandahar ‌da kuma Paktia.

Pakistan ta ce ta kai hare-hare ta sama da ƙasa kan yankunan Taliban da hedkwatar soji da wata cibiyar adana makamai.

Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif, ya ce haƙurinsu ya kare kan yadda Afghanistan ke takalarsu da faɗa, a don haka su ma sun buɗe koƙar yaƙi da maƙwabciyar ta su.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin Pakistan, Mosharraf Zaidi ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, ta ce sun samu nasarar halaka dakarun Taliban kimanin 133, tare da jikkata wasu 200, sannan suka kama 9 daga cikinsu.

Shi ko mai magana da yawun Taliban cewa ya yi sun kashe sojojin Pakistan 55.

Birtaniya, Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumar Agaji ta Duniya wato Red Cross sun yi kira da a gaggauta mayar da wuƙa cikin kube a komawa teburin sulhu.

A nata ɓangaren, Amurka ta bayyana goyon bayanta ga Pakistan, inda mataimakiyar sakatariyar harkokin siyasa ta Amurka, Allison Hooker, ta ce Amurka na goyon bayan haƙƙin Pakistan na kare kanta daga hare-haren Taliban, bayan tattaunawa da wani jami’in Pakistan.

Wannan farmaki shi ne mafi faɗi da Pakistan ta taɓa kai wa Afghanistan tun bayan dawowar Taliban kan mulki a 2021.

Pakistan na zargin Afghanistan da kasa daƙile ƙungiyoyin ’yan bindiga da ke kai hare-hare a cikin ƙasarta, zargin da Taliban ke musantawa.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa yawancin hare-haren dai ƙungiyar Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP) ce ke ɗaukar alhaki, wadda ta ƙara ƙaimi tun bayan dawowar Taliban kan mulki.

’Yan Afghanistan za su kare ƙasarsu — Hamid Karzai

Tsohon shugaban Afghanistan, Hamid Karzai, wanda ya mulki ƙasar daga 2002 zuwa 2014, ya ce ’yan ƙasar za su kare ƙarsarsu.

Cikin wata sanarwa da ya fitar bayan harin na Pakistan, Mr Karzai ya ce “’Yan Afghanistan za su kare ƙasarsu ta hanyar cikakken haɗin kai a kowane fanni, kuma za su mayar da martani kan duk wani hari da aka kai musu cikin ƙwarin gwiwa,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

“Dole ne Pakistan ta sauya ƙudirinta, sanna ta rungumi maƙwabtanta da mutuntawa da girmamawa tare da mu’amala mai kyau,” in ji shi.

Karzai ya kasance cikin manyan ’yan siyasar Afghanistan ƙalilan da suka ci gaba da zama a ƙasar, tun bayan da Taliban ta ƙwace mulkin ƙasar a 2021.

China da Iran sun miƙa tayin shiga tsakani

Tuni dai ƙasashen China da Iran suka miƙa tayin shiga tsakanin domin kawo sasanci a sabon rikicin.

China ta ce ta yi matuƙar damuwa game da tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu.

Cikin wani saƙo da Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta fitar ta yi kira ga duka ɓangarotrin biyu “su kai zuciya nesa tare da warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa.”

Ma’aikatar ta ƙara da cewa China na yin duk mai yiwa domin shiga tsakani ta hanyoyin da suka dace, kuma za ta ci gaba da ƙoƙarin warware rikicin ta hanyar sasanci.

“A matsayin maƙwabciya kuma ƙawa ga duka ƙasashen, mun yi matuƙar damuwa da wannan rikici da har ya janyo asarar rayuka,” kamar yadda Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Chinan, Mao Ning ya bayyana.

A nata ɓangare Iran wadda ake yi wa kallon giwar ƙasashen Larabawa ta ce a shirye take ta shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce ƙasarsa a shirye take ta taimaka wajen “sauƙaƙa tattaunawa” tsakanin Pakistan da Afghanistan bayan da rikici ya barke tsakanin kasashen biyu.

Ya kuma yi kira ga ƙasashen biyu da su “warware bambance-bambancensu ta hanyar kyakkyawar makwabtaka da tattaunawa.”

A baya, Iran ta riga ta yi tayin shiga tsakanin ƙasashen biyu a matsayin mai shiga tsakani yayin da zaman ɗar-ɗar kan iyakar ƙasahen ke ƙaruwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *