Tinubu Ya Jaddada Shirin Gwamnatinsa Na Kafa Ƴansandan Jihohi A Nijeriya


Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin da ta gabata, ya tabbatar wa Ƴan Nijeriya cewa; ƙasar na fita daga ƙalubalen tattalin arziƙi da tsaro, inda ya bayyana cewa; Nijeriya ta fita daga cikin dazuzzuka. Ya kuma yi alƙawarin cewa, ana ƙoƙarin kafa Ƴansandan jihohi, domin magance tashe-tashen hankula a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne, a lokacin buɗa baki da gwamnonin jihohi da mataimakan gwamnoni biyu da manyan jami’ai a fadar gwamnati da ke Abuja.

  • Gwamnatin Bauchi Ta Nemi Agajin Tinubu Game Da Yaƙi Da Ta’addanci
  • Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano

Ya kuma jaddada buƙatar tsayawa tsayin daka da kuma sadaukar da kai ga farfaɗowar wannan ƙasa.

“Sakamakon aiki tuƙuru, shi ne ƙarin aiki, amma muddin muka haɗa kai kuma muka ƙudiri aniyar ceto ƙasar nan, to mafi alherin yana nan tafe.

“Mun fita daga cikin dazuzzuka, mun kuma fita daga cikin duhun rami na rashin tabbas,” in ji shi.

Dangane da rashin tsaro, shugaba Tinubu ya ƙara da cewa; “Ga waɗanda ba su da aikin yi, na yi alƙawarin za mu kafa Ƴansandan jihohi, domin ƙarfafa tsaro a ƙananan hukumominmu.

Ya kuma yi kira da a haɗa kai da sadaukarwa a yayin da musulmai ke gudanar da azumin watan Ramadan, Kirista kuma su ma na yin nasu azumin.

Tinubu ya yaba wa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, bisa shirin ciyarwa a wannan wata na Ramadan, sannan ya buƙaci a ƙara ƙarfafa gwiwar matasa da kuma ci gaban ƙasa.

“Tsaɓi da sadaukarwa da bangaskiya da juriya da azama, suna da muhimmanci a gare mu, mu yi addu’a tare, mu ƙaunaci juna da kuma hidimta wa Ɗan’adam,” in ji shi.

Har ila yau, ya kuma yaba wa gwamnonin, bisa nasarorin da suka samu, inda ya nuna cewa; an samu fitowar jama’a da dama duk kuwa da gudanar da taron jam’iyyar da kuma gudanar da ayyukan cikin gida.

“Na gode wa Allah a kan abin da muka samu tare, mun ga ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukanmu,” in ji shi, yana mai jaddada buƙatar yaɗa ayyukan ci gaba a faɗin ƙananan hukumomi da kuma jawo hankalin matasa.

An gabatar da addu’o’i a wajen taron daga mabiya addinin kirista da kuma na musulmi daga bakin babban Limamin gidan gwamnati Abdulwaheed (Muslim) da kuma gwamnan Taraba Agbu Kefas (Kirista).

Tun da farko, Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda ya wakilci shugaban ƙungiyar gwamnonin Nijeriya, ya yaba wa Tinubu kan samar da haɗin kan ƙasa a cikin rikicin addini da ƙabilanci.

Ya kuma bayyana taron a matsayin wanda Allah ya albarkace shi, yana mai cewa; ba kasafai ake haɗuwa a irin wannan wata na Ramadan da Azumin kiristoci ba, a ajiye bambance-bambance a gefe.

Uzodinma ya yaba wa shugaban ƙasar kan inganta haɗin gwiwa da gwamnoni da kuma ƙarfafa tallafa wa marasa galihu a lokacin azumi.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da mambobin majalisar ministoci da dama sun halarci taron tare da gwamnonin da suka haɗa da Aleɗ Otti (Abia), Dapo Abiodun (Ogun), Babagana Zulum (Borno), Inuwa Yahaya (Gombe), Ahmed Aliyu (Sokoto), Sheriff Oboreɓwori (Delta), Abdullahi Sule (Nasarawa), Abba Kabir Yusuf (Kano), da sauransu.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *