Zaɓen 2027: Abin Da Ƴan Nijeriya Ke Tsammani
A yayin da ƙasar nan ke tunkarar zaɓukan 2027, amma a gefe ɗaya, ƙasar na ci gaba da fuskantar ƙalubalen rashin tsaro, musamman ganin yadda, ayyukan ta’andanci ya ƙungiyoyin Ƴan ta’adda, na Boko Haram da na ISWAP, ke ci gaba da yin ƙamari, a yankin Arewa Maso Gabas.
Kazalika, a wasu sassan jihohin Zamfara, Katsina, Niger, Sokoto, Kebbi da Kwara, ayyukan Ƴan bindiga daji, sai ƙara ta’azaara yake yi.
- Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe
- 2027: Za Mu Kare Kuri’unmu, Ba Za Mu Maimaita Kuskuren Abin Da Ya Faru A 2023 Ba – Peter Obi
Bugu da ƙari, a jihohin Filato da Biniwe, ana ana fuskantar rikice-rikicen ƙabilanci, inda a kuduancin ƙasar, ana fuskantar tashe-tashen hankula, daga gun ‘yaƴan ƙungiyar masu fafutukar a raba Nijeriya wato IPOB da ke a jihohin Kudu Maso Gabas.
Hakazalika, waɗannan matsalilin, na kuma shafar harkar tattalin arziki, wanda hakan ya sanya alumomin da ke a waɗannan jihohin, ke ci gaba dakon kan yaya lamarin zaɓukan na 2027, za su kasance.
Misali, ƙurar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufai ya tayar, a kwanan baya a fagen siyasar ƙasar, ta hanyar kalamansa da ya furta, hakan ya ƙasa rura musayar kalamai, a fagen siyasar ƙasar, musamman duba da cewa, kamalaman na san a zuwa ne, daidai da lokacin da ake tunkrar zaɓukan na 2027.
Abin takaicin shi ne, yadda wasu manyan Ƴan siyasa a ƙasar suka gaza, fahimtar gaskiya.
Wasu furucin da ka aka yi a kafen yaɗa labarai na Talabijin na Abuja, musamman kan ƙaramar hukumar Birnin Gwari, Owerri, Jos, da kuma Yenagoa, hakan ya ƙara dagula al’amuran ƙabilanci da addini ko kuma na yanki.
A ƙasar kamar Nijeriya, da ke fama da matsalar rashin tsaro, sakin baki na furta irin waɗanna kalaman, babbar matsala ce.
A yayin da Ƴan adawa ke danganta gazawa a ɓangaren gwamnati na iya mulki na gari, inda kuma ɓangaren gwamnatin ke yi watsi da wannan iƙirarin na Ƴan adawa, bisa cewa, ana yi mata zagon ƙasa ne, hakan ya ƙara jefa rashin yarda, a zukatan Ƴan Nijeriya.
Amincewa da sakamakon sahihan zaɓukan da aka gudanar a tsakanin Ƴan takara, shi ne, baban hanyar da ke tabbatar da zaman lafiya.
Amma idan jigajigan manyan ƙasa suka nuna shakku kan mahukunta, kuma ba tare da bayyana sahihan hujjojinsu ba, amma suka ɓuge da son cimma wata manufa ta ƙashin kansu, hakan na iya rusa ginshiƙin da ake da aka ɗora ƙasar.
A Nijeriya dai, bay au ne kawai, aka saba ganin irin matsalar rura wutar gabar siyasa da ke kunno kai, tun kafin a gudanar da zaɓuka, a ƙasar ba
Masali, a 2011 ƙasar ta fuskanci rikice-rikice bayan gudanar da zaɓuka, wanda ya rikiɗe, zuwa rasa rayuka.
Ya zama wajbi, mu tashi tsaye, domin kar a sake mai=maita ‘yar gidan jiya, a zaɓukan na 2027.
Dole kuma, jigajigan Ƴan siyasa a ƙasar, su yi takan tsan-tsan wajen kaucewa, hadda rikici, a zaɓukan na 2027.
Bugu da ƙari, dole ne jigajigan Ƴan siyasa a ƙasar, su rinƙa auna furucinsu, kafin ta kaisu, ga furta su, tare da kuma kaucewa yin amfani da magoya bayansu, domin tayar da zaune tsaye.
Wannan nauyin ba wai kawai, ya rataya kan Ƴan siyasa bane, har da a ɓangaren kafafen yaɗa labarai , suma yi hattara da irin rahotannin da za su wallafa, ba tare da sun rura wutar rikici ba.
Kazalka, ya zama wajbi, a sanya ido kan rahotanin da ake wallafawa, a shafukan sada zamunta na zamani domin a kaucewa, yaɗawa alumma, rahotannin Ƙanzon Kurege.
Tuni dai, yanayin tsaron ƙasar ya taɓarɓare, inda duk wani na’uin rikicin siyasa, na iya janyowa, ƙilu ta janyo bau, musamman ta hanyar yaɗa raɗe-raɗi da furta kalamai saka-ka.
Hukumomin tsaron ƙasar, ba za su iya jurewa irin wanna lamarin ba, musamman duba da irin ɗimin barazanar matsalar tsaro.
Wannan Jaridar a ra’ayin mu, muna kira a rinƙa samar da sahihan bayanai, a yayin da ake tunkar zaɓukan na 2027.
Bugu da ƙari, dole ne a tskanin jam’iyyu, da su tabatar da sun samar da wata kafa ta kawar da duk wasu kalamai, musamman a lokacin da suke yin muhawara a kafar Talabjin don kaucewa, yin zafafar muhara, da za ta iya haddasa tashin hankali.