An kashe manoma 15 a wani sabon harin a Filato

[ad_1]



Aƙalla manoma 15 ne suka rasu lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari wasu ƙauyuka bakwai na Chakfem da ke Ƙaramar Hukumar Mangu, a Jihar Filato.

Maharan sun kuma ƙone gidaje da dama, tare da sace dabbobi, yayin da mutane sama da 3,000 suka tsere daga gidajensu.

“Lamarin ya faru ne da daren ranar Litinin tsakanin ƙarfe 7:30 zuwa 8:00,” in ji Bulus Dabit, shugaban ƙungiyar Mwaghavul Development Association (MDA).

“Maharan sun ƙone gidaje da dama ciki har da gidan Sarki da motarsa. Waɗanda bs su gudu ba an kashe su.”

Mutane da dama sun ji rauni kuma an kai su Asibitin COCIN da ke Mwar-Chakfem.

Sarkin yankin, Raymond Yombish ya ce: “Da suka kawo harin, na samu na tsere, amma motata ta gwamnati sun ƙone ta. Wannan lamari ya yi muni sosai saboda yawansu ya yi yawa.”

Wani wanda ya kuɓuta daga harin, Sohotden Emmanuel, ya ce: “Na gudu na ɓuya a gona har sai da suka tafi. Sun zo da makamai masu yawan gaske, kuma adadinsu ya fi ƙarfinmu.

“Mun kasa kare kanmu, Allah ne kaɗai Ya taimake mu. Ina kira ga gwamnati ta ba mu damar kare kanmu.”

An zargi Fulani da kai harin

Mista Dabit ya zargi Fulani da kai harin.

Ya ce: “Manufarsu ita ce su shiga tsakiyar Mangu. Sun zo da yawa ne a wannan karon domin su yi nasara.”

Amma Shugaban Miyetti Allah a Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya musanta zargin.

Ya ce: “Mun yi Allah-wadai da harin kuma muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

“Amma wannan zargi ba shi da tushe. Ba mu da hannu a harin. Ya kamata jami’an tsaro su bincika.”

An nemi gwamnati ta kai ɗauki

Dabit ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta ɗaukar mataki.

Ya ce: “Sai gwamnati ta yi wani abu cikin gaggawa, idan ba haka ba, za a ƙarar da waɗannan al’umma baki ɗaya.”

Har yanzu jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba game da harin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *