Bikin Bazara Na Shekarar Doki Ya Kara Kuzari Mai Karfi Ga Tattalin Arzikin Duniya
[ad_1]
Za a iya bayyana kasuwar Bikin Bazara ta shekarar Doki ta kasar Sin ta bana a matsayin mai “cike da kuzari”, a matsayin sabuwar shekara ta biyu ta kasar Sin bayan da Bikin Bazara ya samu nasarar shiga cikin jerin bukukuwan al’adu da dan’adam ya gada a duniya na UNESCO.
Yayin lokacin hutu na Bikin Bazara, yawan zirga-zirgar fasinjoji da aka yi jigilarsu a sassan yankuna daban daban na kasar Sin ya zarce biliyan 2.8, kana matsakaicin yawan fasinjojin a kowace rana ya kai miliyan 311, wanda ya karu da kashi 8.2% idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara.
Matsakaicin yawan kudin da aka samu a kowace rana wajen sayar da kayayyakin da ba na sari ba, da abinci, da ma abin sha ya karu da kaso 5.7% bisa na makamancin lokacin a bara. Hukumomin bincike na kwastam na kasar sun tabbatar da cewa, mutane miliyan 17.796 sun shiga ko fita daga kasar a lokacin Bikin Bazara, inda matsakaicin adadinsu a kowace rana ya kai miliyan 1.977, wanda ya karu da kashi 10.1% bisa na makamancin lokacin bikin bazara na bara.
Wadannan alkaluman sun kafa kyakyawan mafari yayin da ake fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, inda har ma wata kafar watsa labarai ta Spain ta yaba da cewa, Bikin Bazara na shekarar Doki ya zama abin da ke kara kuzari ga tattalin arzikin duniya.
Musayar mutane tsakanin Sin da sauran kasashe ya zama wani muhimmin bangare yayin Bikin Bazara. A lokacin hutu na bikin, masu yawon bude ido na Sin sun ziyarci birane kusan dubu a fadin duniya. Masu yawon bude ido na kasashen waje su ma sun kai ziyara a Sin don murnar sabuwar shekara, inda yawan odar jiragen sama ya ninka sau hudu bisa makamancin lokaci na bara.
Bikin Bazara na shekarar Doki na kasar Sin mai cike da farin ciki, ya bai wa duniya damar shaida ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Tun daga farkon wannan shekarar, hukumomin kasa da kasa da dama sun daga hasashensu game da tattalin arzikin kasar Sin, kuma sun nuna cewa, za su dora muhimmanci kan habaka zuba jarinsu a kasar Sin. Kwanan nan, kamfanoni da kungiyoyi da dama daga kasashen waje sun raka shugabannin kasashensu a ziyarar aikinsu a kasar Sin, don tsara kasuwanci a kasuwar kasar Sin.
Sabuwar shekara ta kawo sabon yanayi. Kasar Sin za ta yi namijin kokarin samun ci gaba tare da kasa da kasa. (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link