’Yan bindiga sun sace masu ibada 6 a coci a Ondo
Aƙalla mutum shida ’yan bindiga suka sace yayin da suka tsaka da yin ibada a cocin Celestial Church of Christ (CCC) da ke yankin Uso a Jihar Ondo.
Harin ya auku ne da misalin ƙarfe 12:50 na daren ranar Laraba.
’Yan bindigar sun yi ta harbi sama don firgita mutane kafin yin awon gaba da masu ibadar.
’Yan sanda sun tabbatar da faruwar harin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Jimoh Abayomi, ya ce jami’ansu tare da sojoji da ƙungiyoyin sa-kai sun isa yankin don yin bincike.
A halin yanzu, an ceto ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, an kuma kama wani mutum da ake zargin yana bai wa maharan bayanai.
’Yan sanda suna ci gaba da aiki don ceto sauran da aka sace tare da kama maharan.
Abayomi, ya roƙi mazauna garin su kwantar da hankalinsu, su kasance masu sanya ido, kuma su bai wa jami’an tsaro bayanin duk wani da ba su yarda da shi ba.
Wannan lamari ya biyo bayan sace mutane da aka yi a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa, kwana huɗu da suka wuce, wanda hakan ke nuni da ƙara taɓarɓarewar tsaro a yankin.