Kwamitin Kolin JKS Da Majalisar Gudanarwa Ta Kasar Sin Sun Taya Tawagar Kasar Ta Wasannin Olympics Na Lokacin Hunturu Murna
[ad_1]
Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) da majalisar gudanarwar kasar sun aika sakon taya murna ga tawagar kasar Sin a gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2026 ta Milan-Cortina, suna masu yaba mata bisa samun sakamako mafi kyau a wasannin Olympics na lokacin hunturu da aka yi a ketare.
Tawagar ta samu yabo bisa yadda ta samarwa kasar Sin da al’ummarta lambobin zinare 5 da azurfa 4 da tagulla 6.
An kuma bukaci tawagar ta mayar da hankali wajen gina kasar Sin zuwa mai karfi a bangaren wasanni da ci gaba da kai wa sabbin matakai a fagen wasannin hunturu a duniya, ta yadda za ta karfafa da fadada nasarar kasar ta shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin lokacin hunturu. (FMM)
[ad_2]
Source link