Gwamnatin Jihar Gombe Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasar New Zealand Kan Kiwon Dabbobi
Gwamnatin Jihar Gombe da hukumar bunkasa fannin kiwon dabbobi na zamani (LIC) da ke kasar New Zealand, sun rattaba hannun yarjejeniyar bunkasa fannin kiwon dabbobi na zamani tare da kuma kara karfafa jurewar kiwo na kowane irin yanayi da kuma kara samar da wata sabuwar damar haBaka tattalin arzikin da ke fannin na jihar.
Sun kulla wannan yarjejeniyar ce, biyo bayan wata ziyara ta kwana biyu da Gwaman Jihar Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jagoranci wata tawaga zuwa hukumar, inda ziyarar ta bayar da damar kulla wannan yarjejeniya.
- Amurka Ta Kwace Kadarorin ‘Yan Nijeriya 8 Masu Alaka Da Boko Haram
- Kisan Ƙare Dangi: Sojojin Amurka Sun Fara Aikin Samar Da Tsaro A Nijeriya
Isma’ila Uba Misilli, Darakta Janar na yada labaran gwamnan ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar, inda sanarwar ta ce; a karkashin wannan yarjejeniya, Bangarorin biyu za su kaddamar da gudanar shirin bincken hadaka a tsakaninsu, wacce za a sanya jami’ar Jihar Gombe, domin gudanar da binciken, musamman kan yadda za a fito da damar jinsin dabbobi tare da kuma gabatar da sabon tsarin samar da Madarar Shanu da namansu.
Gwamna Yahaya, a jawabinsa a wajen rattaba hannun yarjejeniyar ya danganta hadakar a matsayin mai matukar muhimmanci da kuma girma, musamman domin a kara bunkasa kokarin da gwamnatin jihar ke ci gaba da yi na haBaka fannin kiwon dabbobi.
Ya bayyana cewa, wannan shirin ya yi daidai da irin kokarin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi, na saita fannin kiwon dabbobi na kasar, ta hanyar amfani da ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi ta tarayya.
Shi kuwa a nasa jawabin, babban ministan ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi, Idi Mukhtar Maiha, ya yaba da wannan yarjejeniyar, wanda ya ce; ta zo daidai da irin kokarin da gwamnatin tarayya ke ci gaba yi, na kara bunkasa fannin kiwon dabbobi na kasar, musamman gannin yadda gwamnatin ke da yakinin cewa; yin kiwon dabbobin na zamani, zai kara haBaka fannin a kasar nan.
Shi ma a nasa jawabin, a madadin hukumar Manajan Bunkasa Samar da Madarar Shanu na kasa da kasa, Jason Schrier, ya yi maraba da kulla wannan yarjejeniyar wadda kuma ya danganta ta a matsayin wani mataki na kara haBaka hadakar kasa da kasa, ta bunkasa fannin kiwon dabbobi.
Ya bayyana cewa, a karkashin wannan yarjejeniyar, hukumar za ta kawo kwararru, inda hakan zai kara taimaka wa masu kiwon dabbobi da ke jihar ta Gombe, har na dogon zango.
An dai kafa wannan hukumar ce a shekarar 1909, wadda kuma ta ke ci gaba da zama kan gaba a fannin yin kiwon dabbobi ta hanyar amfani da fasahar kimiyyar zamani.