Miji ya yi wa matarsa yankan rago

[ad_1]



Ana zargin wani magidanci da yanka maƙogwaron matarsa bayan wata sa-in-sa da ta haɗa su a ƙauyen Amaji, yankin Ƙaramar Hukumar Omuma, Jihar Ribas.

Ana zargin Mista Abuchi da matarsa sun yi cacar baki ne tun suna a gona, shi kuma da ransa ya ɓaci, bai yi jinkiri ba ya buga mata wuƙa a maƙogwaro.

Bayan ta faɗi ƙasa warwas, jini na ta kwarara, kafin a yi gaggawar ɗaukar ta zuwa asibiti ta ce: “Ga garinku nan.”

Ɗaya daga cikin dangin mamaciyar ya shaida wa Aminiya abin da ya faru. Ya ce: “Suna gini ne a ƙauyen Amaji da suke, sai wata ’yar rashin jituwa ta gifta tsakaninsu.

“Shi da matarsa suka yi faɗa, shi kuma da ransa ya ɓaci sai ya ɗauki wuƙar da mata ke yanka nama a ɗakin girki ya caka mata a maƙogwaro.

“Nan take ta faɗi ƙasa tana kakari. Abin ya faru kafin jama’a su farga har su kawo mata ɗauki, ta riga ta mutu.”

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ribas, CSP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da lamarin ya faru kuma an cafke magidancin.

Ta ce: “Eh! Tabbas an kamo shi, yana hannunmu. Ana masa tambayoyi kan dalilin da ya sa ya kasa haƙuri ya ɗauki doka a hannunsa ya kashe matarsa.”

“Da zarar an kammala bincike, kotu za ta ɗauki mataki, mu kuma za mu ci gaba da aikinmu,” in ji ta.

Tuni cibiyar da ke fafutukar hana gallazawa da cin zarafin mutane (CBRAC) ta bayyana abin da Mista Abuchi ya yi da matsayin dabbanci wanda babu irin sa.

Ko’odinetan ƙungiyar na ƙasa a Jihar Ribas, Prince Wiro, a sanarwar da ya fitar ranar Juma’a ya ce babu wani uzuri ko hanzari da mijin zai bayar da zai sa shi aikata haka.

Ya ƙara da cewa: “Na yi matuƙar ɓacin rai, kuma Allah wadai da wannan abin kunya na wannan mijin da ya kashe matarsa ba tare da dalili ba.”

“Wannan lamari ya jefa al’ummar ƙauyen da iyalan mamaciyar cikin firgici. Abin kuma ya kamata ya fuskanci hukunci mai tsanani.”

Kakakin rundunar ’yan sandan ta ce: “Da zarar an kammala bincike, kotu za ta ɗauki mataki, mu kuma za mu ci gaba da aikinmu.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *