Ɗan majalisar Kano ya fice daga NNPP zuwa APC

[ad_1]



Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Dala a Jihar Kano, Aliyu Sani Madakin Gini, ya fice daga jam’iyyar NNPP tare da komawa APC.

Madakin Gini, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a majalisar wakilai, ya sanar da hakan cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 10 ga watan Maris, 2026.

Ya aike wasiƙar ga shugaban jam’iyyar NNPP na Unguwar Yalwa da ke Ƙaramar Hukumar Dala ta Jihar Kano.

A cikin wasiƙar, ɗan majalisar ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan tuntuɓar abokan siyasarsa da magoya bayansa a faɗin Kano, musamman a gundumomi 12 da ke mazaɓar Dala.

Ya ce matakin cikin bai zo masa da sauƙi ba, la’akari da irin sadaukarwar da ya yi wa jam’iyyar da kuma tafiyar siyasar Kwankwasiyya.

Sai dai ya ce rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar ne suka sa ya yanke shawarar ficewa.

A cewarsa, jam’iyyar ta rabu gida biyu, inda ɓangare ɗaya ke goyon bayan Boniface Aniebonam, yayin da wani ɓangaren kuma ke goyon bayan tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Madakin Gini, ya ce wannan dalili ne ya sa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar shi da magoya bayansa.

Ya ce: “Ina so na sanar da ku a hukumance cewa daga wannan lokaci ni da magoya bayana kun fice daga jam’iyyar NNPP.”

Ya kuma ƙara da cewa ya koma jam’iyyar APC tare da magoya bayansa a faɗin Jihar Kano.

Idan ba a manta ba, Madakin Gini ya jima da nesanta kansa daga tafiyar Kwankwasiyya, lamarin da ya kai ya daina sanya jan hula wadda ita ce alamar ƙungiyar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *