Ƙoƙarin Amurka Na Ganin An Haramta Shari’a A Nijeriya Ya Haifar Da Cece-kuce

[ad_1]

Malaman Addinin Musulunci da sauran manyan shugabannin al’umma, sun yi fatali da shawarar da wani Kwamitin Majalisar Dokokin Amurka ya bayar, wanda ya buƙaci a soke dokokin Shari’a da kuma dokokin ɓatanci a Nijeriya.

Shawarwarin da ke fitowa daga Majalisar Dokokin Amurkan, wanda ke ƙunshe a cikin wani rahoto na haɗin gwiwa kan “Tsangwamar Kiristoci a Nijeriya”, waɗanda suka haɗa da Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Dokoki da Kwamitin Samar da Kuɗi na Majalisar wanda suka gabatar wa Fadar White House, a ranar Litinin, game da ci gaban tsaro a Nijeriya, sun haɗa da kwance ɗamarar Fulani makiyaya, da hana fitar da naman sa da sauran kayayyakin da suka shafi shanu zuwa ƙasashe kamar Iɓory Coast, Senegal da Ghana.

  • Sin Na Bibiyar Halin Da Ake Ciki Yayin Da Zaman Tankiya Ke Karuwa Tsakanin Amurka Da Iran
  • An Kama Mutumin Da Ya Ƙera ‘Jirgin Annabi Nuhu’ A Ghana

Har ila yau, kwamitin ya yi iƙirarin a cikin rahotonsa cewa; bayan shekaru da dama na zalunci, Nijeriya ita ce; ƙasa mafi muni a duniya wajen zaman Kiristoci, yana mai jaddada cewa; “Kiristoci na fuskantar munanan hare-hare daga mayaƙan Fulani masu ɗauke da makamai da ƙungiyoyin Ƴan ta’adda, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kisan dubban Kiristoci, da suka haɗa da limamai da lalata dubban wuraren ibada da makarantu da kuma yin garkuwa da mutane.

“Ana amfani da dokokin cin zarafi a jihohin Arewacin Nijeriya, domin rufe bakin magana da rashin amincewa, a kai wa kiristoci da tsiraru hari, da kuma ba da hujjar abin da ake kira ‘hukunce-hukunce’ ba tare da bin ƙa’ida ba.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *