Ɗan Kwankwaso ya yi murabus daga kujerar Kwamishina a Kano
[ad_1]
Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya yi murabus daga muƙaminsa na memba a Majalisar Zartarwar Jihar.
Mustapha Kwankwaso ya sanar da murabus ɗin nasa ne a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, inda ya miƙa godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi ta yi wa jihar hidima.
A cikin sanarwar, ya ce ya yi murabus ne “ba don haka ya so ba” yana mai jaddada cewa ya samu darussa masu muhimmanci da gogewa a lokacin da yake gudanar da aikinsa.
Ya kuma bayyana fatan ɓangaren matasa da wasanni zai ci gaba da samun kulawa daga gwamnatin yanzu, tare da kira da a ci gaba da zuba jari wajen bunƙasa matasa da ci gaban wasanni a jihar.
A ƙarshe, Kwankwaso ya yi wa Kano da shugabanninta addu’a, yana mai roƙon Allah Ya ci gaba da yi wa jihar albarka.
Murabus ɗin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake guguwar sauyin sheƙar siyasa ke kaɗawa a cikin gwamnatin Jihar Kano, bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link