Zaɓen Mazaɓu Na APC A Sakkwato Alama Ce Ta Haɗin Kai

[ad_1]

Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen mazaɓu na jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato, Alhaji Lawali Liman Kaura ya bayyana cewar yadda jam’iyyar ta gudanar da zaben ba tare da wata hayaniya ba ya nuna hadin kan da jam’iyyar ke da shi a jihar.

A tattaunawar sa da manema labarai, Kaura ya ce ya gamsu da yadda zaɓen mazaɓu 244 ya gudana a faɗin jihar.

  • Gwamnatin Tarayya Da Gwamnonin APC Sun Ba Da Gudummawar Naira Biliyan 8 Ga ‘Yan Kasuwar Singa
  • Rikicin Kabilanci A Jihar Ribas Ya Tayar Da Hankalin Al’umma

Shugaban kwamitin ya ce yadda manbobin jam’iyyar suka nuna halaye nagari a yayin zaɓen ya nuna alamar tambarin jam’iyyar na tsintsiya wanda ke nuna haɗin kai.

A kan wannan ya buƙaci dukkanin manbobin jam’iyyar da su ci gaba da nuna halaye nagari a yayin zaɓen jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *