Zargin Almundahana: Kwamitin NAHCON Ya Kaɗa Ƙuri’a Kan Neman A Kori Shugabanta

[ad_1]

Kwamitin Gudanarwa na Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ya kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da Shugaban hukumar, Abdullahi Saleh Usman, bisa zargin karkatar da kuɗaɗe, take dokoki, gazawar shugabanci da kuma dagula dangantakar Nijeriya da Saudiyya.

A cikin wata takarda koke mai kwanan wata 19 ga watan Janairu, 2026, da aka aike wa Shugaba Bola Tinubu, kwamitin ya ce matakin ya biyo bayan dogon lokaci na lura da al’amura da kuma ƙoƙarin gyara da ba su haifar da sakamakon da ake so ba.

  • Tsaro: Gwamnatin Nijeriya Ta Ɗauki Rayukan Mutane Da Muhimmanci – Peter Obi
  • ’Yan Bindiga Sun Sace Mutane Sama Da 20 A Katsina

Kwamitin ya zargi shugaban da amincewa da kashe kuɗaɗe da bayar da kwangiloli ba tare da sahalewar kwamitin ba, tare da wuce abin da aka ƙayyade a kasafin kuɗi, wanda ya saɓa wa dokokin kuɗaɗen gwamnati.

Takardar ta kuma bayyana cewa hukumar EFCC na bincike a kan shugaban a halin yanzu.

Haka kuma, kwamitin ya yi zargin take dokar Hukumar Kula da Saye-da-Sayarwa ta Ƙasa (BPP), inda ya ce an bayar da wasu kwangilolin aikin Hajji ba tare da bin ƙa’ida ba, ciki har da rashin samun takardar “No Objection” da doka ta tanada.

Dangane da hulɗar ƙasa da ƙasa, kwamitin ya ce wasu zarge-zargen da suka shafi cin hanci sun janyo koma baya a dangantakar Nijeriya da Saudiyya, lamarin da ya sa aka rage wa Nijeriya adadin kujerun maniyyata daga 95,000 a Hajjin 2025 zuwa 50,000 a Hajjin 2026.

Kwamitin ya kuma zargi shugaban da gazawa wajen shugabanci, inda suka ce akwai gazawa wajen tafiyar da harkokin hukumar.

Bisa waɗannan dalilai, kwamitin ya yi gargaɗin cewa ci gaba da zaman shugaban a kan kujerar na iya kawo cikas ga shirye-shiryen Hajjin 2026 tare da jefa Nijeriya cikin matsalolin diflomasiyya, tare da roƙon shugaban ƙasa da ya shiga tsakani don magance matsalar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *