Zan goyi bayan duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa a ADC — Atiku
[ad_1]
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa a shirye yake ya mara wa duk wanda ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC, domin fafatawa a zaɓen shekarar 2027.
Atiku, wanda yana ɗaya daga cikin masu neman tikitin takara a jam’iyyar, ya tabbatar da cewa zai karɓi sakamakon zaɓen fidda-gwani ba tare da wani haufi ba.
Ya kuma yi watsi da raɗe-raɗin da ake yi na cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) na ƙoƙarin daƙile ci gaban ADC.
Y bayyana cewa jam’iyyar na ci gaba da samun karɓuwa da sabbin mambobi a faɗin ƙasar nan.
Idan za a tuna, hukumar INEC ta dakatar da shugabancin jam’iyyar ADC ɓangaren David Mark, tare da ƙin sanya ido kan babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga watan Afrilu.
INEC ta ce ta ɗauki matakim biyo bayan hukuncin kotu kan rikicin cikin gida da ke damun jam’iyyar.
Sai dai, jam’iyyar ADC ta yi watsi da wannan mataki, inda ta zargi INEC da fassara hukuncin kotun ba daidai ba.
Yayin wata hira da ya yi da sashen Hausa na DW, Atiku, ya bayyana cewa wasu ne ke haddasa matsalolin da jam’iyyar sakamakon yadda tauraronta ke ƙara haskawa.
Game da batun tikitin takarar shugaban ƙasa kuwa, Atiku ya jaddada cewa: “Za mu goyi baya tare da amincewa da duk wanda ya zama ɗan takara.
“Mu nawa ne ma (masu neman takarar shugaban ƙasa), uku ko huɗu? A jam’iyyar PDP, mutum sama da 10 ne suka fafata.”
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa jam’iyyar ADC ta matasa ce da mata, inda ya nuna gamsuwa da yadda matasa ke shiga cikinta don tsayawa takara.
“Matasa sun karɓi jam’iyyar. Yawancin masu neman muƙamai daga kan kansila zuwa majalisar jiha, majalisar tarayya da kuma majalisar wakilai, matasa ne.
“Mun daɗe muna cewa jam’iyyarmu ta matasa da mata ce. Aikinmu shi ne samar musu da dama mu miƙa musu ragamar jagoranci.”
Lokacin da aka tambaye shi ko zai amince ya marawa matashi baya idan aka tsayar da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku, ya ce a shirye yake ya amince.
“Eh, me zai hana? Allah Ya riga ya yi min komai. Na dawo da ’ya’yana da jikokina gida. Me zai zama makomarsu da ta ’ya’yanku?”
Hakazalika, ya bayyana cewa ’yan Najeriya na matuƙar buƙatar sauyi sakamakon matsin tattalin arziƙi da kuma taɓarɓarewar tsaro da ake fuskanta a ƙasar nan.
“Muna da tabbacin cewa ’yan Najeriya na marmarin samun sauyi. Sun shirya yin hakan. An matsa musu ƙwarai, kuma a shirye suke su yi abin da suka yi a zaɓukan da suka gabata.”
Atiku, ya alaƙnta ƙaruwar rashin tsaro a Arewacin Najeriya da rashin aikin yi da kuma ƙarancin ilimi a tsakanin matasa.
“Rashin tsaro ya fi tsanani a jihohin Arewa, galibi saboda rashin aikin yi a tsakanin matasa da kuma rashin samun ilimi. Idan ka zagaya yankin, za ka ga cewa ilimi ba ya samun kulawar da ya kamata.
“An mayar da shi baya. Gwamnatoci ba su tabbatar da cewa yara sun shiga makaranta ba, kuma ko da sun kammala, babu ayyukan yi ko damar kasuwanci. Ban taɓa gani lokaci irin wannan ba a Najeriya.”
A ƙarshe, ya soki gwamnati mai ci da rura wutar cin hanci da rashawa a cikin harkokin ƙasa.
“Ana wawure kuɗi daga ɓangaren gwamnati, kuma cin hanci da rashawa ya yi ƙamari. Gwamnati ta rufe ido saboda ita ma tana da hannu a ciki.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link