’Yan sanda sun daƙile harin ’yan bindiga, sun ceto mutum 25 a Zamfara
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Kuraje da ke gefen birnin Gusau.
Wasu gungun ’yan bindiga, ɗauke da makamai ne, suka kutsa cikin ƙauyen suna harbi, lamarin da ya jefa mazauna Kuraje da maƙotan ƙauyukan cikin tashin hankali.
A yayin harin, sun yi awon gaba da mata 10 da yara 15.
Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce ’yan sanda sun ɗauki mataki bayan samun kiran gaggawa.
Ya ce tawagar haɗin gwiwa daga sashen Damba, Sashen Ayyuka da kuma Rundunar Tsaron Al’umma (CPG) sun isa ƙauyen cikin gaggawa.
Sun bi sahun ’yan bindigar, sannan suka yi artabu da su.
’Yan sanda sun ceto dukkanin mutum 25 ba tare da kowa ya ji rauni ba.
An kai matan da yaran zuwa Sabon Gari Damba domin kula da su, kafin su da iyalansu.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya yaba wa jarumtar jami’an da suka yi aikin, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link