‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 11 Yayin Da Ake Kallon Ƙwallo A Mexico
[ad_1]
‘Yan bindiga sun buɗe wuta kan jama’a da ke tsaka da kallon wasan ƙwallo a wani yanki na tsakiyar ƙasar Mexico, inda suka kashe mutane 11 tare da jikkata wasu 12.
Magajin garin Salamanca, Cesar Prieto, ya ce harin ya faru ne kusa a daidai lokacin ƙarshen wasan, lokacin da ‘yan bindigar suka shiga filin suka fara harbi.
- Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Fashi da Makami A Abuja, Sun Kama Wani Mutum
- Ƙwace Mulki A Hannun Tinubu Ne Kaɗai Hanyar Ceto Nijeriya A 2027 — ADC
Wasu daga cikin waɗanda suka jikkata na karɓar kulawa a asibiti, yayin da har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.
Mahukunta sun ce suna zargin miyagun ƙungiyoyi masu safarar ƙwayoyi ne ke da hannu a wannan hari, kasancewar ta’addanci na ƙaruwa a wasu sassan ƙasar.
Mexico na cikin ƙasashe uku da za su karɓi baƙuncin wasu daga cikin wasannin gasar cin kofin duniya, lamarin da ke sa mutane nuna damuwa kan tsaro.
[ad_2]
Source link