Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Mutane 19 A Ƙauyen Katsina Da Tsakar Rana
[ad_1]
A ranar Talata, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a garin Doma da ke gundumar Tafoki a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, inda suka kashe akalla mazauna 19, a cewar majiyoyin yankin.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar, wadanda ke dauke da muggan makamai, sun mamaye al’ummar da tsakar rana kuma sun yi ta tafka ta’asar na tsawon awanni biyu.
Wani mazaunin yankin, wanda ya tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin, ya ce maharan sun yi ta kewaye cikin gari tsakanin misalin karfe 12:00 na rana zuwa 2:00 na rana, suna duka tare da kashe mazauna yankin.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin da aka kai a gundumar sanatan Katsina ta Kudu ba.
[ad_2]
Source link