Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Ginin Ma’aikatar Noma Da Ya Laƙume Naira Biliyan 7
[ad_1]
A shekarar 1966 ne, aka ƙirƙiro da ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci ta tarayya, wacce kuma ta fuskanci sauye-sauyen suna da dama tare da garanbawul da gwamnatocin baya suka yi.
Sai dai, shekara 30 da ta gabata, bayan sauya wa ma’aikatar matsuguni daga Jihar Legas zuwa babban birnin tarayya Abuja, ba tava samun wata shalkwata tata ta kanta ba.
A halin yanzu dai, ma’aikatar ta kasance ne a ginin hukumar tafiyar da birnin na Abuja, wadda ta kasance tana da bene mai hawa uku kacal tare da kuma rashin samar mata da wadatattun sassan gudanar da ayyuakanta.
- Yawan Hatsin Da Kasar Sin Ta Noma Ya Kai Wani Sabon Matsayi Na Koli A 2025
- Dalilin Manoma Na Rungumar Irin Farin Wake A Jihar Benuwe
Ma’aikatar, wadda a 2018 ƙarƙashin tsohon ministanta, Cif Audu Ogbeh, ana kiranta ne da ma’aikatar bunƙasa aikin noma da raya karkara, inda a wancan lokacin aka sayi wani gini da ke cibiyar kasuwanci a Abuja, kan naira biliyan 7 a matsayin shalkwatar ma’aikatar, wanda ginin ya kasance mai bene hawa takwas.
shalkwatar, wanda aka saya a lokacin tsohowar shugabar ma’aikata ta tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esan, ya haifar da ƙura da ke ƙunshe a cikin wata takardar gargaɗi da aka miƙa wa babban sakataren ma’aikatar, Dakta Mohammed Bello, wanda ya sanya ido wajen sayen ginin.
An dai miƙa masa takardar gargaɗin ce, a ranar 11 ga watan Mayun 2020, wadda aka umarce shi ya yi bayani a cikin sa’o’i 72, kan batun sayen ginin a matsayin shalkwatar ma’aikatar.
Takardar gargaɗin dai, ta tuhumi babban sakataren kan sanya ido wajen sayen ginin, ba tare da abin ƙa’ida ba.
Sai dai, bayan sayen shalkwatar, an gano cewa; gini ne da ba a riga an kammala shi ba.
Amma, a martanin da Dakta Bello ya bayar kan batun sayen shalkwatar ya sanar da cewa, an gabatar da buƙatar sayen ginin ne, wanda kuma tsohon ministan Cif Ogbeh, ya gabatar wa da wani kamfani, inda kuma ya gabatar da batun a zaman da majalisar zartawa ta yi, kan buƙatar amincewa da sayen ginin.
Tun bayan tsawon waɗannan shekaru, ginin ya kasance a matsayin wanda aka yi watsi da shi, wanda kuma aka mayar da shi wajen ajiye motocin ma’aikatar.
Sake Amincewar Gwamnatin Tarayya Na Sayen Wani Ginin:
A watan Afirilun 2023, majalisar zartarwa ta sake amincewa da yi wa shalkwatar ma’aikatar kwaskwarima, duk a matsugunin na ma’aikatar.
Tsohon ministan da ke sanya ido kan tafiyar da ma’aikatar, Mohammad Abubakar, a wata hira da manema labarai, ya shaida musu cewa; majalisar zartarwar ta amince da kashe naira biliyan 6, domin fara yi wa sabuwar shalkwatar ma’aikatar kwaskwarima.
A cewar Abubakar, sabuwar shalkwatar, za ta kasance tana da bene mai hawa 10, wadda aka sanya wa suna ‘Agriculture House.’
Abubakar ya ƙara da cewa, mahukuntan birnin na Abuja, sun samar da wani gini a yankin ‘Cadastral’, wanda ke da faɗin hekta guda 1.84.
Ya ci gaba da cewa, dalilin da ya sanya aka yi watsi da ginin na kimanin naira biliyan 7 shi ne, an gano cewa; wajen ya yi kaɗan, sannan kuma ba zai ɗauki sauran sassa na ma’aikatan ba.
Ya ƙara da cewa, an tsara za a sayar da ita, domin a zuba kuɗin a cikn kasafin kuɗi na tsakanin 2022 zuwa 2023, a kan naira biliyan 6, domin a fara gudanar da sabon aikin shalkwwatar.
An Keve Sama Da Naira Biliyan 5 A Kasafin Kuɗi Na 2026:
A cikin kasafin kuɗi na 2026, an keve naira biliyan 5.67, domin gyaran shalkwatar ma’aikatar.
Wannan adadin, ya kai jimillar naira biliyan 11.67, da aka amince, domin sayen sabuwar shalkwatar ma’aikatar.
Shekaru takwas bayan yunƙuri na farko, har zuwa yanzu, ma’aiaktar ba ta kai matakin shalkwata ba.
Ma’aikatar Ta Kashe Naira Biliyan 2026:
Duk da naira tiriliyan 58.18 da gwamnatin tarayya ta zuba a cikin kasafin kuɗi na 2026, ma’aiktar da kuma hukumomin aikin noma da ke ƙarƙashinta, sun samu jimillar naira tirliyan 1.44 ne kacal.
Idan aka yi duba kan jeren ayyuakan da kuma irin ɗimbin kuɗaɗen da aka keve wa ma’aikatar, a cikin kasafin kuɗi na 2026, ƙididdiga ta nuna cewa, yarjejeniyar da aka ƙulla ta ƙasa da ƙasa da ke cikin bashin shiri na musamman na bunƙasa aikin noma a shiyyoyi shida na ƙasar, wato SAPZ, za su laƙume kimanin naira biliyan 126.02.
[ad_2]
Source link