Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
[ad_1]
Daga zamanin Annabi Idris mala’iku ne suka kawo sako suke yin magana da mutanen kasa, su ake cewa tatsuniyoyi na duk al’umma (tatsuniya ne a wajenmu amma su gaske ne a wajensu), su ce mutane sun sauko musu daga sama, har aka zo zamanin Annabi Nuhu ya tabbatar, da ya zo ya fada wa mutane suka ce ba su yarda ba, ba mu ji wannan wajen iyayenmu ba, haka aka ci gaba har zuwa zamanin Annabi Hudu dan Adam ya fara hore dabbobi, dabbar da dan Adam ya fara horewa shi ne kare, kuma ya hore dabbobin da zai ci, zai iya gane wannan dabbar ba zai ci ba, wannan zai ci, wannan zai iya zama da ita lafiya, wannan ba zai iya zama da ita ba, daga nan dan Adam ya fara gini, ya dan kwakule kasa ya yi kogo ya shiga.
Har ya zuwa Annabi Salihu, har dan Adam ya fara fahimtar wannan kwayar da take fitowa a kasa, wannan zan iya ci in rayu, wannan kwayar kuma ba a cin ta, har ya soma tunanin toh wannan kwayar ya zan ajiye ta zuwa nan gaba in sake shuka ta, haka dan Adam har ya soma yin noma a aikace don ya rayu. Allah ya gaya mana wannan yana daga cikin ayoyin Allah (kamar yadda ya zo a aya) “arziki yana daga cikin kasa da abin da kasa take tsirarwa da abin da hannunka yake aikatawa” kamar sana’a ko noma ko nema. Toh ka ga a nan babu zancen ka ce ba za ka yi nema ba, duk abin da kake nema idan ka juya kasa za ka same shi, duka kasar da ta rike noma da sana’a za ku ga sun fi arziki, Allah ga shi ya gaya mana idan kafiri ya fi ka arziki sai dai ka nema a wajensa, don haka mu dogara da Allah shi ke azurtawa, ga ka’idoji nan ya fada mana, nema, kiwo abubuwa duk gabaki daya.
Toh zamanin Annabi Salihu ne aka yi wannan, dan Adam ya iya noma, har aka zo lokacin Annabi Shu’aibu dan Adam har ya kai yana zuba hatsi cikin buhu, har ya kai yana awo. Annabi Shu’aibu ya zo da ka’idojin awo na kar ka cuci wanda za ka auna wajensa, kar a cuci wanda za a auna wa, har duniya ta ci gaba aka soma rubutu, da rubutun duniya sai dai idan buhu goma za ka karba kai kuma ka ba da rago guda daya toh kai sai ka yi hoton ragon nan (shi “drawing” rubutun kowa ne, ilimin kowa ne, da kurma da bebe da jahili idan ka yi mai “drawing” ya sani). Toh yanzu kai sai ka zana abu kamarsa guda daya ma’ana na ba shi saniya guda daya, shi kuma sai ya zana buhu kamar guda goma haka aka dinga ban-gishiri-in-ba-ka-manda kafin a soma fito da “hardcopy” na rubutu wanda aka fara rubutu da shi. Har yanzu akwai mutanen da za ka ga akwai “drawing” a cikin rubutunsu bare Misirawa din nan, to sannan rubutu ne irin na kasuwanci.
Sai bauta kuma haka, masu gina dakin bauta dole za su iya rubutu saboda za a kawo abubuwan kyauta na dakin bauta duk za a rubuta wannan abu, ba rubutu ne ba hotonsu za a yi, wannan shekara dubu uku kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) toh har Allah ya sa Misrawa suka fito da “ABCD” su ma mutanen Iraki suka fito da nasu, mutanen Yemen suka fito da nasu shi ma nau’i ne na karatu, aka soma rubutu yanzu ba wancan “drawing” din ba iya rubuta komai an iya karantawa, tun daga zamanin rubutu duniya ta soma canzawa, an soma rubuta tarihin sarakuna da dai sauransu, har duniya ta ci gaba da gine-gine kuma na kwatance, ka samu ilimi na gine-gine, duniya ta iya gina dalar gyada ta Misra da dakunan bauta, da gine-ginen da har yau an rasa ya aka yi aka yi su, har mutane na cewa aljanu ne suka gina, a’a mutane ne, amma abin mamaki duniya ta rasa wai ya aka yi suka yi wannan fentin nan da ya zauna shekara dubu goma ruwa na dukansu, dari na dukansa, zafi na dukansa amma fentin nan bai goge ba, amma mu yanzu ko “original” fenti ka siyo idan za a yi shekara daya sai ka ga wajen na bukatar fenti, wai ya aka yi haka? Meye wannan suka hada? Kuma fenti ne ga shi.
Yanzu wannan dalolin an rasa ya aka yi su, ta ina ma aka zo da wadannan duwatsu, ya aka yi aka kai su sama duk da an ce wai mutane ne manya, duk karya ne domin da mun ga kasusuwansu, Samudawa mutane ne masu karfin jiki ba wai manya ba ne sosai, da an ga kasusuwansu, tsabar himma ce kawai ko yanzu idan ka yi himma za ka yi abubuwan da za a ce aljani ne. Tun daga Babila har Iraki har Misra har Yemen din duk gaba daya har aka zo zamanin Annabi Ibrahim (AS) ya zo ya gina mana Ka’aba, ya gane fahimtar duniya canzawa take yi Hanafiyya, duniya ba waje daya take ba, shi har ya zama ma duka abin da za a ce “Permanent” ne zai ce sai Allah.
Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna tsoron wanda zai yi tunani a gaba, saboda duk wanda ya kawo wani ilimi sai ka ji an ce Zindiki ne, sai a so a halaka shi ma idan ba a yi wasa ba. Toh abin da ya dinga faruwa kenan har Allah Ya kawo falasfawa na Greeks Socrate, wasu sun ce Annabi ne, suka zo suka canza ilimi shi kan shi wannan Socrate din kashe shi aka yi da aka ce ko ya ce bai yarda da wannan ilimi ba, ko ya sha dafi shi kuma ya ce Allah ba zai ba shi ilmi ba, don haka gwara ya sha dafi ya mutu ya yarda ya sha, ga shi su wanda suka kashe shi ba sunansu shi kuwa har yau sunansa a duniyar ilimi ba zai bace ba. Toh Allah kuma Ya kawo juyin juya hali daga karni na 1800 har ya zuwa 1900 ilimin ya soma yalwata da aka fara rubuta shi, wasu na cewa ba mahaukaci sai wanda ya ba da aron littafi, ba wanda ya fi shi hauka sai wanda ya dawo da shi, wannan a lokacin da ake rubuta littafi da hannu kenan amma yanzu ya kare, an ce Shehu ya zo gidan daya daga cikin shehunnanmu yana duba library sai ya ga wani littafi sai ya ce ka ga wannan littafi na neme shi ban samu ba, ba ni aro sai ya ce Shehu na ba ka aro dauki, sai Shehu ya ce masu hikima sun ce babu mahaukaci sai wanda ya ba da aron littafi, ba wanda ya fi hauka sai wanda ya dawo da littafi, ya ce ni dai ba zan zama mahaukaci ba, sai Shehu ya yi masa wasa.
To da aka soma rubutun, China kamar su suka soma, to da buga littafi ilimi ya soma ya)uwa zuwa ga jama’a, ilimi ya fito daga dakin bauta, ya fito daga masarautar sarakuna ya shiga gidan kowa, a da kuwa yana gidan sarakuna ne kawai, ilimi ya soma yaduwa har Allah ya kawo Rediy,o tana daga cikin abin da ya yada ilimi, ta yi hobbasa wajen wayar da kan komai, dan haka a kula da rediyo yana da matukar kyau saboda galibin mutane rediyon nan ita ce hanyar daukar maganarsu, Allah ya saka wa Shehu Ibrahim Inyass (RA) da alkhairi, ya sha wahala wajen sa karatun Kurani a ciki, har Allah ya kawo talabijin, har “cable” din nan ta zo, yanzu fa za ka iya ganin duniya a cikin abu, karshen wayewa, karshen ci gaba a yanzu kuma wayar salula, wadannan wayoyi da suke hannunmu sun sa a yanzu babu jahili sai dai dakiki wanda ya ki sani da gangan, amma wayar nan babbar farfesa ce ta kowane karni, idan fannin jinya ne za ta fada ma har abin da hankalinka ba zai taba kawowa ba, haka a fannin alheri, idan fannin tarihi ne za ta kai ka har inda kudinka ba zai iya kai ka ba. Alhamdu Lillah, mun gode Allah.
[ad_2]
Source link