Wani ya kashe ɗan uwansa saboda ya harbe shi a mafarki

[ad_1]



An kama wani mutum mai shekaru 43 a duniya a garin Sepeteri na Jihar Oyo, bisa zargin kashe babban yayansa, Mustapha Amidu, bayan ya yi zargin ya harbe shi a mafarki.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ayanlad Olayinka ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Ibadan.

Ya ce an kai rahoton lamarin hedikwatar ’yan sanda ta Ago-Amodu daga wani mutum mai suna Badmus Yunisa na unguwar Alegunlode a yankin Sepeteri.

A cewarsa, wanda ake zargin ya je inda marigayin yake zaune, ya ɗauki wani babban dutse ya buga masa a kai sannan ya tsere.

An garzaya da marigayin zuwa asibitin Ileri-Oluwa da ke Sepeteri, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Olayinka, ya ce bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin shugaban ofishin Ago-Amodu sun ziyarci wajen da lamarin ya faru da kuma asibitin domin fara bincike.

Ya ƙara da cewa an kama wanda ake zargin, kuma ya amsa laifin, yana kuma ba ’yan sanda haɗin kai wajen gudanar da binciken.

Ya kuma ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Femi Haruna, ya bayar da umarnin a mik5a lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar (SCID) domin ci gaba da bincike.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *