Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Ƙaddamar Da Tallafin Abincin Azumi Da Sallah Ga Mutane 16,000

[ad_1]

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Lawal, ta ƙaddamar da raba tallafin abincin Azumi da Sallah ga marayu da marasa galihu a faɗin jihar Zamfara.

Da take jawabi a taron da aka gudanar a Gusau ranar Asabar, Huriyya Lawal ta ce, shirin zai amfani mutane 16,000 da aka tantance waɗanda za su sami buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25, tallafin kuɗi na ₦20,000, da kayan Sallah, a Karkashin Masarautu 19 da ke cikin Jihar ta Zamfara.

  • Ramadan: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci Ga Limamai 40 A Zamfara
  • ’Yan Jarida Da AGILE Sun Ƙulla Haɗin Guiwar Ƙarfafa Ilimin ’Ya’ya Mata A Sakkwato

Waɗanda zasu amfana sun haɗa da marayu, zawarawa, da iyalai waɗanda ke cikin buƙata.

Uwargidan gwamnan ta bayyana alƙawarin Gwamnati na inganta jin daɗin jama’a masu rauni a faɗin jihar. Ta ƙara da cewa, a baya shirye-shiryen sun haɗa da tallafawa Auren marayu mata da tallafin kasuwanci

Uwargidan gwamnan ta yaba wa Hukumar Zakka da Wakafi wajan jajircewarta tsara wannan tallafin ga marasa galihu, kuma ta yi kira ga waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da tallafin da yadda ya dace.

Shirin wani bangare ne na kokarin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na rage wahalhalu da kuma inganta dogaro da kai a jihar.

A cikin jawabinsa, Sakataren zartarwa na hukumar Zakka,Alhaji Habib Muhammad Balarabe, ya ce taron shiri da gwamnatin jihar ta yi don tallafawa marayu da masu bukatu na musamman da ke cikin mawuyacin hali.

Ya nuna godiyarsa ga Gwamna Dauda Lawal bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar da kuma jin dadin al’ummar da ke cikin mawuyacin hali.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *