Tsaro: Kwamitin Majalisar Ƙasa Ya Yi Watsi Da Kasafin Kuɗin Rundunar Sojin Sama Na 2026
[ad_1]
Kwamitocin haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Kasa kan rundunar sojin sama ta Nijeriya, a ranar Talata sun yi watsi da shawarar kasafin kudin rundunar sojin sama ta Nijeriya na 2026, duba da cewa, akwai rashin isassun kudade da kuma kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
An yanke wannan shawara ne a lokacin zaman kare kasafin kudi da Kwamitin Majalisar Dattawa da na Wakilai kan rundunar sojin sama suka gudanar tare, inda shugabannin rundunonin suka gabatar da yadda suka gudanar da ayyukan kasafin kudin rundunar na 2025 da kuma shirin kasafin 2026.
Shugaban kwamitin hadin gwiwa kan rundunar sojin saman, Sanata Osita Ngwu, ya sanar da sakamakon zaman da cewa, ‘yan majalisar sun yi watsi da shawarar kasafin kudin da rundunar sojin ta gabatar.
Ya ce, kwamitin ya yanke wannan shawara ne bayan cikakken nazari kan kiyasi da kuma gaskiyar lamari kan kalubalen tsaro da ke ci gaba da wanzuwa a fadin kasar.
[ad_2]
Source link