Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake duba albashin ma’aikata
[ad_1]
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ma’aikatan gwamnati, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta sake duba mafi ƙarancin albashi, domin Naira Naira 70,000 da ake biya yanzu ba ta isa wajen tafiyar da al’amuran yau da kullum.
A cewarsu tashin farashin kayan abinci, sufuri, haya, da wutar lantarki ya ƙara jefa su cikin wahalar da rayuwa.
A wasu jihohi kamar Imo, Legas da Ribas sun riga sun ƙara mafi ƙarancin albashi sama da wanda gwamnatin tarayya ke biya.
Mista Benson Upah, Sakataren riƙo na NLC, ya ce: “Naira 70,000 ba za ta iya ɗaukar nauyin rayuwa a wannan yanayi na tattalin arziƙi da ake ciki ba.
“Ma’aikata na cikin matsin lamba sosai, kuma idan gwamnati ba ta ɗauki mataki cikin gaggawa ba, matsalar rayuwa za ta ƙara tsananta.”
Shi ma shugaban ƙungiyar manyan ma’aikata, Mista Shehu Mohammed, ya jaddada buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa.
“Idan mutum ya biya kuɗin wuta daga Naira 70,000, abin da ya rage ba zai iya ciyar da iyalinsa har tsawon kwana goma ba. Gwamnatin Tarayya dole ta yi saurin ɗaukar mataki.”
Ma’aikata na buƙatar gwamnati ta ƙara albashi tare da aiwatar da manufofin da za su rage tsadar rayuwa a Najeriya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link