Trump Ya Yi Kira Ga Iraniyawa Su Fara Yunƙurin Sauya Gwamnati

[ad_1]

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya buƙaci al’ummar Iran da su yi amfani da halin da ƙasar ke ciki wajen yunƙurin sauya gwamnatin da ke mulki.

A cikin wani saƙon bidiyo da ya fitar, Trump ya bayyana cewa hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai sun buɗe wata dama ga ’yan Iran domin su nemi sauyin shugabanci a ƙasarsu.

  • Sin Na Bibiyar Halin Da Ake Ciki Yayin Da Zaman Tankiya Ke Karuwa Tsakanin Amurka Da Iran
  • Wane Taimako Rasha Da China Za Su Bai Wa Iran Idan Ta Fara Yaƙi Da Amurka?

Ya ce bayan kammala matakan da ƙasashen suka ɗauka, lokaci ya yi da al’ummar Iran za su ɗauki mataki domin ƙwace makomar ƙasarsu.

Har ila yau, Trump ya yi kira ga sojojin Iran da su ajiye makamansu, yana mai cewa za a ba su kariya idan suka amince da hakan, amma ya gargaɗe su da cewa rashin yin hakan na iya jefa su cikin haɗari.

Tun a farkon watan Janairu ne tsohon shugaban na Amurka ya fara nuna fushinsa kan yadda hukumomin tsaron Iran ke mu’amala da masu zanga-zangar adawa da gwamnati, lamarin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama suka ce ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

Kalaman na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa da na tsaro ke ci gaba da ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya, abin da ke ƙara jawo hankalin ƙasashen duniya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *