Tinubu ya san dalilin da ya sa na yi murabus daga muƙamin ministan — Badaru

[ad_1]



Tsohon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya san dalilin da ya sa ya yi murabus.

Badaru, ya ajiye aiki ne a ranar Litinin, inda ya ce matsar rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus.

Shugaban ƙasa ya amince da murabus ɗinsa kuma ya naɗa Janar Chris Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro.

Badaru, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya yi murabus ne saboda barazanar da Amurka ta yi na ɗaukar matakin soji kan Najeriya game da zargin kisan Kiristoci.

“Ina so na bayyana a fili cewa wannan labari ƙarya ne, an ƙirƙire shi don ɓata min suna, kuma ba shi da alaƙa da ni ko wani da ke magana a madadina,” in ji shi.

Ya ce an ƙirƙiro wannan ƙarya ne don a ɓata masa suna da kuma haddasa rikici tsakaninsa da shugaban ƙasa.

“Gaskiyar dalilin murabus ɗina na bayyana ta shugaban ƙasa. Duk wani ƙarin bayani na daban ƙarya ne da aka ƙirƙira,” in ji Badaru.

Ya tabbatar wa Tinubu da ’yan Najeriya cewa har yanzu yana biyayya, tare da jajircewa wajen ganin an samu zaman lafiya, tsaro da nasarar jam’iyyar APC kafin zaɓen 2027.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *