Tinubu ya buƙaci majalisa ta tsawaita wa’adin kasafin 2025 zuwa Maris 2026

[ad_1]



Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci Majalisar Tarayya da su soke tare da daidaita kasafin kuɗin shekarar 2024 da na 2025.

Haka kuma ya nemi a tsawaita aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 har zuwa ranar 31 ga watan Maris, 2026.

Tinubu, ya bayyana hakan ne cikin wasiƙar da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, wadda aka karanta a zaman majalisar na ranar Juma’a.

Ya ce ana buƙatar sake duba kasafin kuɗin ne domin haɗa abubuwan da ba a sanya a baya ba, da kuma daidaita kasafin da halin tattalin arzikin ƙasa a yanzu.

A cewarsa, tsawaita kasafin kuɗin 2025 zai bai wa gwamnati damar sakin ƙarin kuɗaɗe don gudanar manyan ayyukan ci gaba kamar gina hanyoyi, wutar lantarki da sauran ayyuka.

Ya ce hakan zai taimaka wajen inganta tsari da amfani da kuɗin jama’a yadda ya kamata.

Shugaban ya ƙara da cewa wannan mataki zai rage matsalar tafiyar da kasafin kuɗi sama da lokaci guda, tare da ƙara gaskiya da riƙon amana wajen kashe kuɗin gwamnati.

Ya roƙi ’yan majalisar da su gaggauta duba buƙatar tare da amincewa da ita.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *