Shugaban hukumar ba da tallafin karatu na Kano ya ajiye muƙaminsa

[ad_1]



Shugaban tafiyar Kwankwasiyya kuma Babban Sakataren Hukumar Ba da Tallafin Karatu ta Jihar Kano, Dokta Hamisu Musa Gambo, ya ajiye muƙaminsa.

Dokta Gambo ya sanar da hakan ne cikin wata wasiƙar bayyana murabus mai kwanan watan 27 ga Janairu, 2026, wadda ya aike wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar.

A cikin wasiƙar, Gambo ya bayyana cewa matakin nasa yana da alaƙa da ficewar gwamnan daga jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya zuwa APC, lamarin da ya ce ya saɓa wa matsayinsa da aƙidarsa ta siyasa.

Ya jaddada cewa har yanzu biyayyarsa da jajircewarsa na nan daram a jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Kano kuma babban jigo a jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

“Wannan mataki nawa ya biyo bayan sauye-sauyen siyasa na baya-bayan nan, musamman ficewar Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP da Kwankwasiyya zuwa APC da Gandujiyya,” in ji wasiƙar.

Sai dai duk da murabus ɗin nasa, Dokta Gambo ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi ta yin aiki a gwamnatinsa, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne cike da girmamawa ga ofishin gwamnan.

Haka kuma, ya yaba wa ma’aikata da shugabancin Hukumar Ba da Tallafin Karatu ta Kano bisa haɗin kai da goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake kan muƙamin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *