Saƙon Kirsimeti: Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su rungumi zaman lafiya

[ad_1]



Yayin da mabiya addinin Kirista ke murnar haihuwar Annabi Isa a yau, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu tare ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya da ƙaunar juna.

Shugaban Ƙasa ya sake jaddada kudurinsa na juriya da fahimtar addinai, yana mai cewa babu wani ɗan Najeriya da za a tilasta ya sha wahala ko ya mutu saboda akidar addininsa.

A cikin saƙon Kirsimeti da ya fitar a ranar Laraba, Shugaban Ƙasa ya jaddada cewa juriya da fahimtar addinai na daga cikin manyan dabi’un ƙasa da ke ɗinke Najeriya wuri guda duk da bambance-bambancen da ake da su.

“Babu wanda ya kamata a tilasta ya sha wahala saboda kabilarsa ko addininsa a Najeriya,” in ji Tinubu.

Ya ƙara da cewa:“Ƙaunar Allah da ƙaunar ɗan Adam suna zuciyar dukkan manyan addinai. Waɗannan dabi’u na bai daya dole su ci gaba da ɗaure mu a matsayin tsinstiya madaurinki daya guda a matsayin al’umma ɗaya mai ƙarfi da juriya a ƙasarmu mai albarka.”

Wannan shi ne saƙon Kirsimeti na uku da Tinubu ya fitar tun bayan darewarsa kan mulki a watan Mayu 2023.

Sakon nasa na zuwa ne a daidai lokacin da aka sanya wa matsayin Najeriya dangane da ’yancin addini ido a duniya.

A ranar 31 ga Oktoba, 2025, Shugaban Ƙasa na Amurka Donald Trump ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kallon suna da matsaloli masu tsanani kan ‘yancin addini, yana mai cewa “Kiristanci na fuskantar barazana a Najeriya” tare da zargin cewa “masu jihadi ne ke da alhakin kisan gilla.”

Sai dai Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan Najeriya na yin ibada cikin ’yanci.

Tinubu, wanda Musulmi ne amma matarsa Kirista ce, ya nuna cewa tun bayan darewarsa kan mulki ya kasance yana tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa ba za ta yi wasa da tsaron ƙasa, haɗin kai da zaman lafiya ba.

Tinubu ya kuma yi jinjina ga Kiristocin Najeriya bisa gudummawar da suke bayarwa wajen ci gaban ƙasa.

“Yayin da muke murnar haihuwar Yesu, mu yi tunani kan gagarumar gudummawar da Kiristoci suka bayar kuma suke ci gaba da bayarwa wajen ci gaban ƙasarmu,” in ji shi, yana mai cewa saƙon Almasihu ya zaburar da mutane da dama wajen kula da marasa ƙarfi da talakawa.

Shugaban Ƙasa ya bayyana Kirsimeti a matsayin lokacin shauki, yana tunatar da ’yan kasar cewa “duk da manyan ƙalubale, Allah yana tare da mu.”

Ya yi wa Kiristoci a Najeriya da duniya barka da Kirsimeti tare da addu’ar zaman lafiya, musamman tsakanin mabiya addinai daban-daban.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *